Labarai
Haryanzu Nageriya Bata shirya kafa ‘yan Sandan Jihohi ba ~Sufeto Janar.
Sufeto Janar na ‘yan sandan ya bayyana cewa har yanzu Najeriya ba ta shirya kafa ‘yan sandan jihohi ba.
Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa, Najeriya ba za ta fara yin shirin kafa ‘yan sandan jihohi ba a Yanzu
Ben Okolo, mataimakin sufeto-janar na ‘yan sandan ne ya bayyana haka, Egbetokun ya jaddada cewa Najeriya ba ta da isasshiyar shirye-shiryen aiwatar da ‘yan sandan jihohi.
Ya ce, tsarin Shugabancin Yan sandan Najeriya har yanzu Najeriya bai wadatu da fara shirin kafa ‘yan sandan da ke karkashin ikon jihohi.”