Labarai

Himmata da kokarina yasa muke samun nasara kan COVID19~Ganduje

Spread the love


Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce jihar tana kan nasarori Mista Abba Anwar, Babban Sakataren yada labarai na gwamnan, ya ce Ganduje ya fadi hakane a wata sanarwa a ranar Asabar a jihar  Kano. Sanarwar ta ce gwamnan ya yi wannan furucin ne a yayin wani taron manema labarai na Rundunar Tsaro ta jihar a kan COVID-19. Ganduje ya ce an cimma nasarar ne saboda kwazon da yake nunawa da kuma himmarsa wajen jagorantar matakin yaki kan cutar ta COVID-19.
Gwamnan Ya bayyana cewa samfuran COVID-19 da aka samu a cikin jihar sun fi karfin Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) data kafa. Gwamnan ya ce: “Yayin da NCDC ke sanya maki 100 na tarin samfuri a kowace jiha, tarin samfurin jihar Kano ya kai dari.  “Idan aka tattara samfurori da gwaje-gwajen da suka fito daga gare su, hakika muna cin nasarar yaki da COVID-19 a cikin jihar Kano.”  Dr Tijjani Hussaini, kwamandan Rundunar Tsaro ta Fasaha na jihar kan yaki da COVID-19, yana mai cewa jihar tana da cibiyoyin gwajin kwayoyin halittu guda biyar don inganta ganowa da kuma kyakkyawan tasirin cutar. “Saboda yawan samfuran da aka tara a cikin jihar sun ninka abin da NCDC ta bada, har yanzu muna dauke da wasu samfuranmu zuwa Abuja don gwaji.” Kamfanin dillancin labaran Ink ya labarta cewa, ma’aikatar lafiya ta jihar ta sanar da cewa, kawo yanzu jihar ta gudanar da gwaje-gwaje samfurin CVID-19 13,727, tun bayan barkewar cutar. Ma’aikatar ta sanar da hakan ne a  shafin ta na Twitter @KNSMOH, cewa an gwada samfuran kamar a ranar Juma’a, 3 ga Yuli. Ya ce an tabbatar da sabbin kwayoyin cutar guda biyar daga cikin samfuran 809 da aka gwada a ranar Jumma’a, yayin da karin marasa lafiya 26 na COVID-19 suka fice. Ma’aikatar ta sanar da cewa jihar ta kunshi mutane 1,262 da aka tabbatar sun kamu da cutar; daga cikinsu 207 muna karabar magani Yayinda mutun 1,003 suka warke  mutun 52.kuma mun mutun kawo yanzu…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button