Kunne Ya Girmi Kaka

Hujjojin Dake Nuna Asalin Hausawa Daga Misira Suke.

Spread the love

Daga Littafin ‘Gamsasshen Asalin Hausawa Da Harshensu’ Wanda Comrade Zakariyya Abdurrahman Shu’aibu Kabo Ya Wallafa A Shekarar 2013.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo.

Kashi Na ɗaya.

SALSALAR BAHAUSHE
Marubucin wannan littafi ya tafi akan cewa:- Jinsin Zangiy ɗan Nuhu sune mazauna Afirka ta yamma da tsakiyar ta da kuma Kudancinta.

Sai dai dangane da masu danganta cewa jinsin bakin mutum ya fito ne daga Hamu ɗan Annabi Nuhu A.S wannan kuskure ne, har suke cewa wai an samu saɓani ne sai Annabi Nuhu yayi masa addu’a shine har ya koma baki, a sakamakon haka kuma duk zuriyatasa ta zamo bakake.

Marubucin yace :- Hakika Malamai sunyi raddi akan haka, ga abinda babban malamin tarihin nan Ibn Khaldun ke cewa game da batun “Hakika waɗansu daga cikin masu nasabta abu waɗanda suke basu da ilimi dangane da kasantuwar halittu suna kawo ruɗu da cewa wai bakake ‘ya’yan Hamu ne ɗan Nuhu..

A karshe sai yake cewa wannan hikaya ce daga kissoshi masu kurakurai.

Amma dangane da addu’ar da Nuhu yayiwa ɗan nasa, Ibn Kaldun yace kissar tazo a cikin littafin Attaura, amma babu wata magana da ta nuna ya koma baki, sai dai Nuhu yayi addu’ar wa ɗan nasa ne don ya zama karamin bawan ‘yan uwansa, amma ba ya canza launin fata ba.

Bayan ɗaukewar ruwan ɗufana, sai Zangiy ya zauna a garuruwan farko na afirka, domin wajen nada albarkar noma.

Haka kuma Baban namu na bakaken fata, ya zauna a gefen kogin Nilu na kasar misra wanda kogine mai tarihi wanda ke cikin kogunan farko da Allah ya soma halitta kuma asalinsa daga kasar Uganda yake, sannan ya shigo Somaliya, eritrea da Jubuti kuma ya hauro sudan ya shigo garuruwan Nubia da suke a karkashin hukumar Asuwan ta kasar misira har a karshe ya haɗe da tekun daya wuce Iskandariya duk a kasar ta misira.

Yawan jimawar sa anan yasa kabilu daban daban suka fita daga gareshi, ciki kuwa har da Hausawa..

Dangane da dalilin watsuwar bakaken fata izuwa wannan yanki na afirka, marubucin ya tafi akan cewa Rashin zama lafiya ta dalilin mulki ne ya sanya mutane suka rinka baro danginsu.

Misali, idan uba ya mutu yabar ‘ya’yansa huɗu, a cikinsu sai suka shiga rigimar neman mulki wanda a karshe sai ɗaya ya samu nasara akan yanuwansa, to sai kaga ragowar sun tashi da iyalinsu sun shiga duniya. Don haka yace, a haka bakaken fata suka fantsama har zuwa sassan Najeriya, wasu kuma tun tale -tale sun shiga falasɗinu da sauran garuruwa domin yin kasuwanci, amma kabilar Nubiya itace bata baro misira ba, kuma har yanzu tana misira da zama a karkashin jahar Aswan.

ASALIN HAUSAWA DA DANGINSU
kabilar hausa nadaga cikin kabilun bakaken Afirka ‘ya’yan Zangiy kenan wanda ya rayu a Misira bayan ɗaukewar ruwan ɗufana.

Saboda haka asalin hausawa mazauna Misira ne waɗanda kuma suka rinka gudanar da harkokinsu acan, musamman noma, kiwo da kasuwanci.

Daga bisani sai wani yanki na tushen ƙabilar Hausa ya taso izuwa garuwan Habasha musamman yankin Dahalak, wanda yake cikin kasar Eritrea ayau. Shi wannan yanki na Dahalak har yanzu akwai hausawa masu yawa acikinsa, daga baya ne larabawa suka shiga suka zauna tare da hausawa a cikinsa.

An samu waɗansu mutane guda uku da suka fito daga waɗancan hausawa mazauna dahalak tare da iyalansu izuwa afirka ta yamma. Mutanen kuwa sune Dala, Rano, da Gaya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button