Labarai

Hukuma EFCC ta Kai samame gidan Sanata Abdullahi Adamu Tsohon Shugaban jam’iyar Apc na Kasa.

Spread the love

Hukumar EFCC cike da manyan motoci hudu ne suka dirka gidan shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu mai murabus, a jiya da dare kan tuhume-tuhumen da ake mishi.

A lokacin da suka isa gidan nashi dake Abuja an yi hatsaniya sosai tsakanin ‘yan sandan gidan nashi da jami’an hukumar EFCC, a karshe dai jami’an EFCC din basu samu damar shiga gidan nashi ba.

Kafun a jiye shugabancin na Abdullahi Adamu yasha tsananin matsin lamba daga fadar shugaban kasa da manyan shugabannin jam’iyyar akan lallai sai ya sauka daga mukamin nashi wanda a karshe ya hakura ya ajiye.

A wata majiya da muka samu daga jaridar Peoples Gazette ta ce tun bayan zaben shugaban kasa, fadar shugaban kasa take son ta kori Abdullahi Adamu saboda bai goyi bayan Tinubu ba a lokacin zaben fidda gwani jam’iyya wanda ya gudana a shekarar da ta gabata.

Haka zalika a zaben shugaban kasa ma bai goyi bayan Tinubu ba, duk da anje yawon kamfen kowace jiha tare dashi, wannan dalilin yasa suka ga bai chanchanta ya rike shugabancin jam’iyyar ba. Shima sakataren jam’iyyar na kasa Senator Omisore ya ajiye mukamin nashi.

Manema labarai sun tuntubi Abdullahi Adamu yace ba zai ce komai ba, har sai Tinubu ya dawo Najeriya. A yanzu haka Abdullahi Adamu yana tsaka mai wuya inda hukumar EFCC ke farautarshi.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button