Addini

Hukumar Aikin Hajjin Adamawa Ta Mayar Da Miliyan N53 Ga Mahajjata 46 Da Suka Yi Niyyar Hajjin Shekarar 2020.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Hukumar Kula da Mahajjata ta Jihar Adamawa ta mayar da kudi N53,035,000 ga mahajjata 46 da suka nemi hakan.

Hukumar ta yi hakan ne tun da an dakatar da aikin Hajji a sanadiyyar barkewar cutar Coronavirus.

Mista Salihu Abubakar, Babban Sakatare kuma Babban Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Mahajjata ta Jihar Adamawa ya mayar da kudin da aka ware don aikin hajjin, a ranan Alhamis a Yola.

Babban sakataren zartarwa ya ce kwatankwacin N53,035,000 ne kwamatin ya mayar wa wadanda suka nemi su a maida masu kudin aikin Hajjin shekarar 2020.

Abubakar ya ce jimilla mutane 1,169 suka yi niyyar aikin hajjin daga jihar, sun biya kudin aikin haji mai tsarki na 2020 zuwa Saudi Arabiya.

“Dubu dari shida da casa’in da hudu (694) daga cikin kudin sun biya cikakken kudin N1,459,000 yayin da sauran alhazai 475 ba su cika biyan kudin ba.

“Kuma 46 daga cikin mahajjatan sun neman a maida masu kudinsu,” in ji Abubakar.

Ya ce neman maida kudin, zaben su ne, domin wadanda ba su nemi kudin din ba, za a yi musu rajista kai tsaye don aikin Hajji na shekarar 2021.

Sakataren zartarwa ya ce “Hukumar ta fara shirye-shiryen aikin Hajji na 2021 ne tare da wadanda ba su karbi kudaden su ba,” in ji Sakataren zartarwa.

A cewarsa, hukumar ta ba da sanarwar wata guda ga mahajjata shirin shekarar 2020 don neman dawo masu da kudin su wanda zai kare a yau.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button