Tsaro

Hukumar DSS ta bankado wani shiri da wasu jama’a ke yi na tada rikicin addini a kasar nan.

Jami’an tsaron farin kaya DSS sun bayyana cewa wasu mutane na kokarin tada rikicin addini a kasar nan a kowanne lokaci daga yanzu.

A wata takarda da ta fito daga hannun kakakin hukumar ta DSS Dr Peter Afunanya, ya tabbatar da cewa jami’an su na kokarin shawo kan lamarin don bawa ‘yan Najeriya kariya.

A cikin takarda Dr Peter Afunanya ya lissafo jihohin da masu son tada tarzomar sukafi maida hankali.

Jihohin sun hada da sokoto kano Kaduna plateau Rivers Oyo Lagos da wasu na kudu maso gabashin Najeriya.

Dr Peter Afunanya ya ce daya daga shirin su shine yin amfani da sahun sojoji wajen kai hari guraren bauta da shugabannin addinai, manyan mutane da sauran su.

Don haka hukumar ta DSS take shawartar mutane da su kula sosai a daidai lokacin da hukumar ta DSS ke kokarin hada kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

Daga Kabiru Ado Muhd

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button