Labarai

Hukumar EFCC ta damke wata Mata Mai suna Patience Robert da Laifin damfara a Matsayin jami’ar EFCC.

Spread the love

Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, a shiyyar Makurdi, ta fada a ranar Laraba cewa ta cafke wata mai suna Patience Robert, wacce ake zargi da sojar Gina a matsayin jami’ar EFCC tare da damfarar mutane da dama ta Hanyar sama musu aiki a Hukumar Kwastam ta Najeriya. A wata sanarwa da shugaban yada labarai na hukumar, Wilson Uwuajare, ya ce an kama Robert din ne bayan wani korafi da wani yayu Kan ta karbar Masa N1.5m da nufin za’a taimaka masa a samar wa yaransa ayyukan yi a EFCC.

Sanarwar ta lura cewa mai shigar da karar ya bayyana cewa wacce ake zargin ta yaudari kaninsa ta raba shi da N300,000 bayan ta yi alkawarin sanya yaransa aiki a hukumar ta NCS. Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin zagon kasa ta ce bincike ya nuna cewa sau da yawa ‘yan sanda da sauran hukumomi sunsha kama wanda ake zargin da laifin yin zamba.

“An gano cewa an gurfanar da ita a gaban wata kotun majistare da ke Minna, Jihar Neja, bisa laifin yin zamba da kuma samun kudi ta hanyar karya. Ana zargin ta samu sama da N11m daga hannun wasu da dama da abin ya shafa ta hnayar gabatar musu tabbacin sama masu ayyukan yi a wasu hukumomi, yayin da take nuna kanta a matsayin ma’aikaciyar EFCC. “Wanda ake zargin ta kuma damfari wani a Abuja har kusan N4.5m yayin da take gabatar da kanta a matsayin‘ Daraktar Leken Asirin ’a EFCC,” in ji hukumar ta EFCC. Uwuajare ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button