Labarai

Hukumar EFCC ta saki Ortom bayan shafe sa’o’i 9 yana amsa tambayoyi

Spread the love

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta saki tsohon gwamnan jihar Benuwe, Mista Samuel Ortom, bayan shafe sa’o’i 9 a hannunsu.

Ortom ya isa harabar hedikwatar hukumar dake Makurdi da karfe 10 na safe kuma ya bar wurin da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Talata.

Da yake mayar da martani, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Terver Akase, ya ce sabanin yadda ake ta zarge-zarge a wasu sassan kafafen yada labarai, ba a kama Ortom ba sai dai ya mutunta gayyatar da hukumar ta yi masa.

“Ba a kama shi ba ko kuma aka tsare shi a hedikwatar shiyya ta EFCC da ke Makurdi ba,” inji Akase.

A cewarsa, tsohon gwamnan ba shi da wani abin boyewa, inda ya kara da cewa zai kasance a ko da yaushe domin amsa tambayoyi daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

“Ortom ba shi da wani abin boyewa game da shugabancinsa a jihar,” in ji Akase.

NAN

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button