Labarai

Hukumar EFCC Tayi kira ga A Kafa Kotun Shara’ar Cin Hanci.

Spread the love

Mukaddashin Shugaban Hukumar yaki da Cin hanci da rashawa ta EFCC, Umar Abba Mohammed yakira da a kafa Kotu ta musamman da zata rika shara’a kan masu cin Hanci da Rashawa.

Mohammed yayi wannan kiran ne Jiya Juma’a a Abuja, Lokacin da Komitin sanya Ido ta (ACJA) suka kai masa ziyarar Aiki.

Inda yaci gaba da cewa, “babban kalubale da muke samu a fannin cin hanci da rashawa, kotuna na tafiyar hawainiya wajen yanke hukunci kan masu laifin cin hanci da rashawa, amma Idan (ACJA) ta kirkiri kotu na musamman da zai kula da Shara’ar masu rashaw to komai zai tafi yadda ya kamata.

Kwamitin sanya ido ta ACJA karkashin jagorancin Mrs. Chukuemeka Nweka ta Yabawa Hukumar EFCC ta kuma amince da tsare-tsaren da hukumar ke kai a yanzu.

Nweka da tawagarta sun zagaya lungu da sakon Hukumar inda tace, Hukumar tana da kayan aiki masu inganci kuma tana aiki tukuru wajen yakar Rashawa da yayiwa kasar nan Katutu Inji Ta.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button