Hukumar Hisbah Ta Hana ‘Yan Mata Amfani Da Wayoyin Hannun Da Sanye Tabarau A Kaduna..
Jami’an Hisbah a jihar Kaduna sun hana ‘yan mata a Kauyen Kuriga da ke karkashin Karamar Hukumar Chikun amfani da wayar hannu da tabarau.
A cewar Jaridar SaharaReporters, wani mazaunin garin ya tayar da hankali game da karuwar ayyukan take hakki na Hisbah a yankin.
Ya yi zargin cewa Hisbah na ‘bata ran matasa a Kuriga kuma galibi suna aiwatar da hukunci mai tsauri kan gazawar ɗabi’a’.
“Hisbah tana hukunta matasa saboda sanya gashin baki kuma wani lokacin takan hada har da duka.
“Sun kuma hana mata da‘ yan mata amfani da wayoyin zamani, suna masu cewa ana amfani da shi ne wajen yada dabi’un da ba na addinin Islama ba.
Suna kawai tsoratar da mu ne, ”kamar yadda ya fada wa Jaridar SaharaReporters.
Wani mazaunin garin kuma ya ce ma’aikatan Hisbah sun hana mata da ‘yan mata amfani da tabarau.
“Har ila yau wani lokacin sukan mamaye gidajen da ake gudanar da bukukuwa tare da hukunta kunna kade-kade, raye-raye da kowane irin nishadi,” in ji shi.
Hukumar Hisbah a kwanan nan ta sanya kanun labarai game da aske gashin mata na samari a cikin garin Kano, tana kame mutane saboda sanya suturar da ba ta dace ba tare da kwace babura masu hannu uku daga masu hawa da sanya hotunan da ake ganin na batsa ne sun saba koyarwar addinin Musulunci.
Jaridar Daily Times ta ruwaito cewa hukumar Hisbah ta Kano ta kama masu tuka keke napep uku kan hotunan batsa da kuma aske “askin da ba na Musulunci ba”.