Rahotanni

Hukumar karbar ‘korafe ‘korafe ta jahar Kano ta ci gaba da bincikenta Akan tsohon Sarki, in ji Ganduje

Spread the love

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ba da tabbacin hakan ne ga Hukumar yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano za ta ci gaba da bin diddigin tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II,

“Lokacin da muke son gabatar da shugabanci, gyara ga masarautunmu na gargajiya, tsohon Sarkin bai ba da hadin kai ga ayyukan kawo sauyi ba.saboda Tsarin da aka yi ya lalace, don haka zabin daya rage a gare shi shi ne neman hanyar kare kansa

Ganduje ya sanar da hakan ne a taron tattaunawar da aka yi da kafafen yada labarai da aka gudanar a Africa House, Gidan Gwamnati, Kano, A yau Litinin.

Bayan ya yi bayani kan rashi batun lamuran doka da ke kawo cikas ga tsarin garambawul a lokacin, wajen tabbatar wa jama’a da kuma karfafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar, cewa “Hukumar mu da ke yaki da cin hanci da rashawa za ta ci gaba da bincikar tsohon Sarkin kan al’amuran da yake dasu.

Lokacin da ya kai su kotu don dakatar da Hukumar daga nemansa, an soke karar. Saboda haka za su ci gaba da binciken shi bisa ka’idar doka. ”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button