Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta Nuna Goyon Bayanta Bisa Tsarin Mayar Da Almajirai Jihohinsu..
Daga Miftahu Ahmad Panda.
Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta Kasa (NHRC), Ta Bukaci Da a Cigaba Da Aiwatar Da Tsarinnan Da Gwamnonin Jihohin Arewacin Kasarnan Suka Bijiro Dashi Na Mayar Da Almajirai Jihohinsu Na Haihuwa, Duba Da Irin Halin Da Almajiran Suke Shiga a Lokacin Da Suke Gararamba a Jihohin Da Ba nasuba Dasuke Zuwa da Zummar Karatu Inda Daga Bisani kuma Lamarin Yakan Canza Salo Su Buge Da Barace – Barace Da Gararamba Akan Tituna.
Wannan Lamari Na Mayar Da Almajiran Jihohinsu ya taso ne Duba Da Yadda Aka Samu Barkewar Annobar Cutar Sarkewar Numfashi Ta Covid – 19, wadda a yanzu Haka Ta Fantsama Tareda Cigaba Da Kama Daruruwan Almajiran Da Suke Gararambar Neman Abin Da zasuci batareda Daukar wasu Matakan Kariya ba, Inda da Zarar Daya daga Cikinsu ya Kamu Da Annobar yakanje ya Sakawa ‘Yan Uwansa.
A Sakon Da Hukumar Ta Fitar a Birnin Tarayya Abuja, Wadda Maigirma Sakataren Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta Kasa, Mr. Tony Ojukwu, ya Sakawa Hannu, Hukumar Ta Kara da Cewa “Kaso Mafi Yawa Na Almajiran Suna Fama Da Hadarin Kamuwa Da Cututtuka, Yin Safararsu, Garkuwa Dasu Domin Karbar Kudin Fansa, Sannan Sukan Iya Fadawa Cikin Hadarin Shaye – Shaye, Ta’addanci, Fadace – Fadace, Zinace – Zinace, Sannan a wasu Lokutanma Anayi musu Aure suna ‘Yan Kananu, Da Sauran Irin Makamantansu, Wanda Hakan Abune Da Yake Da Illa Matuka”.