Hukumar Kula Shan Miyagun Kwayoyi Ta Jihar Kano Ta Kama Tone 8.7 Na Miyagun Kwayoyi.
Hukumar da Sha dakuma fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya reshen jihar kano ta bayyana cewa ta Kama Ton Dubu takwas da Dari bakwai na Miyagun Kwayoyi a jahar kano.
Shugaban Hukumar Ibrahim Abdul shine ya bayyana hakan a yau, Albarkacin ranar yaki da shaye-shaye da majalisar dinkin duniya ta ware.
Ibrahim Abdul ya bayyana cewa sun Kama wadannan Kayan ne a lokacin da ake zaman gida na kulle, wanda akayi shigo da Kayan zuwan cikin jihar kano.
Majalisar dinkin duniya ta ware wannan Rana a matsayin ranar yaki da shaye-shaye ta duniya.
Sai dai masu sharhi na ganin cewa shaye-shayen ya samo asali ne daga tsananin rashin aikinyi da ake fama dashi a Najeriya.
Inda suka nunarda cewa 85℅ na mahaukatan Najeriya sun sami matsalar ne sanadiyar shaye-shaye.
Haka lamarin ya shafi Matasa maza da mata, Sannan akwai matan aure dake fama da wannan dabi’ar.
Kuma sun bayyana muddin ana bukatar shawo kan wannan lamari, dole a nemawa Matasa aikin yi.
Daga Abdullahi Muhammad Maiyama