Hukumar Lura Da sauka da Tashin Jirage Ta Rage Albashin Ma’aikata
Hukumar Lura Da Filayen Sauka Da Tashin Jiragen Sama Ta Ragewa Ma’aikatanta Albashi
Daga Miftahu Ahmad Panda
Biyo Bayan Raguwar Samun Kudaden Shiga A Daukacin Hukumomin Gwamnatin Kasarnan Bisa Illar Da Annobar Covid – 19 tayiwa tattalin Arzikin Kasarnan, Hukumar Lura Da Filayen Sauka Da Tashin Jiragen Sama Ta Kasa FAAN, ta Bayyana Cewar Daga Wannan Watan na Mayu Da Muke Ciki Hukumar Bazata iya biyan Ma’aikatanta Cikakken Albashinsu ba, Saboda haka Hukumar Zata Rage Albashin Ma’aikatanta Daga Wannan Watan Na Mayu Da muke Ciki har Zuwa Lokacin Da Komai Zai Dai – Daita,
Sannan Hukumar Ta Tabbatar Da Cewar Da Zarar Abubuwa sun Dawo Dai - Dai a Hukumar to kuwa Babu Shakka Zata Biya Ma'aikatan Dukkannin Hakkokinsu,
Hukumar Ta Bayyana Hakane a Wani Internal Memo Da Tafitar Mai Lambar FAAN/HQ/ADMIN/202005 a Jiya Talata 19 Ga Watan Mayu, Mai Dauke Da Sa Hannun Shugaban Gudanarwar Hukumar M.D. Musa,
Anyiwa Memo Din Dai takene Da "Notice On Payment Of Staff Salary" Memo Din ya Bayyana Cewar An dauki Wannan Matakin ne Domin kubutar Da Hukumar Daga Kalubalen Rashin Kudaden Shiga Da take Fama dashi Sakamakon Dakatar Da Harkokin Sufurin Jiragen Sama a Fadin Kasarnan,
Haka Zalika Sanarwar Ta Bayyana Cewar Za’a cigaba da biyan Kananun Ma’aikata Cikakken Albashinsu, Yayinda Manyan Ma’aikata Masu Matakin Albashi Na 10 Zuwa Sama Za’a Dinga Biyansu Kaso 30 Zuwa 50 Na Cikakken Albashinsu.