Labarai

Hukumar NAFDAC Ta Rage Kudin Yin Rijista Ga Masu Kananan Sana’o’i Da Kashi 80

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

Hukumar Lura Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Kasa NAFDAC, Ta Bayyana Cewar Ta Rage Kaso 80 Na Kudin Da Masu Kananan Sana’o’i Suke Biya Domin yiwa Sana’o’insu Rijista, a Matsayin Wani Bangare Na Biyayya Ga Umarnin Gwamnatin Tarayya Kan Cewar a Saukaka Harkokin Kasuwanci, Domin Ragewa ‘Yan Kasuwa Radadin Matakan Da Ake Dauka Domin Dakile Yaduwar Annobar Covid – 19 a Fadin Kasarnan.

Datake Jawabi a Lokacin Kaddamar Da Tsarin Ragin Daraktar Hukumar Ta NAFDAC, Farfesa Christianah Adeyeye, Ta Bayyana Cewar Tsarin Zaiyi Aikine a Daukacin Shiyyoyin Kasarnan Guda Shida Da Muke Dasu Tareda Birnin Tarayya Abuja, dakuma Jihar Lagos, Farfesa Christianah Ta Kara Da Cewar Kudin Da Za’a Ragewa Masu Kananan Sana’o’in Kuwa Sune Kudin Rijista dakuma Kudin Rijista Ta Yanar Gizo a Tsarin Hukumar Na NAPAMS.

Sannan takara Da Cewar Hukumar Bazata Karbi Ko Sisi a Hannun Masu Kananan Sana’o’i 200 Da Suka Fara Zuwa Domin Yiwa Kasuwancinsu Ko Kananan Kamfanoninsu Rijista ba, Daga Ranar Da Aka Kaddamar Da Wannan Tsarin.

Daga Karshe, Adeyeye Ta Karawa Masu Kananan Kamfanoni Tareda Masu Kananan Sana’o’i Kwarin Guiwa, Ta Hanyar Bukatarsu Da Suzo su Sabuntawa Kamfanoni Tareda Sana’o’in Nasu Rijista Ta Hanyar Tsarinnan Na MSME.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button