Uncategorized
Hukumar NCDC Ta Yi Kira Ga Dr Sule Lamido Da Ya Killace Kansa.
Daga Kabiru Ado Muhd
Hukumar dake kula da dakile cututtuka wato NCDC tayi kira ga tsohon gwamnan jigawa Dr sule lamido da ya gaggauta killace kansa kuma za azo ayi masa gwajin cutar corona virus.
NCDC tace dalili shine Dr sule lamido Na daya daga cikin mutanen da suka hadu da mutumin da ya kamu da cutar a kano.
Don haka hukumar ta bukaci sule lamido da ya killace kansa har Na tsahon sati biyu 2.
Allah ya sauwake