Labarai

Hukumar NDLEA Ta Yi Babban Kamu.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta gano wani sindukin kwantena dauke da kwayoyin tramadol da wasu magunguna da aka haramta amfani da su, a tashar jirgin ruwa ta Brawal da ke Legas.
Babban jami’in ma’aikatar, Harkokin Hulda da Jama’a na hukumar, Mista Jonah Achema, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.

A cikin sanarwar, shugaban, NDLEA, Kanal. Muhammad Abdallah mai ritaya ya ce wannan ya zo ne biyo bayan bin diddigin da ‘yan sanda suka yi na sake kama wani kwantenan dauke da abin taje kai, katan 40 na tramadol da wasu haramtattun kwayoyi.

“Zaku tuna cewa ‘yan sanda masu bincike a yankin Apapa na jihar Legas sun kama wani kwantena mai kafa 40 dauke da kwayoyi da ake zargin tramadol da codeine ne a ranar 6 ga watan Agusta.

“An kama kwantenan a ruwa kuma an dauke ta zuwa tashar jirgin ruwa na Apapa.
“Binciken na NDLEA ya kara bayyana wani kwantenan mai tsawan na kafa 40. Wannan binciken hadin gwiwa ya nuna katan 255 na nau’ikan tramadol da sauran magunguna da aka haramta.

“Binciken na NDLEA ya kara nuna cewa an hada tramadol din ne a Pakistan wanda hakan wani sabon abu ne da aka gano ga hukumar saboda ana kirkiro tramadol a Indiya ne.

“Abdallah ya lura cewa wannan bincike babban ci gaba ne ga hukumar wanda ke bayyana sabuwar hanyar shigo da tramadol zuwa Najeriya wacce ta kasance daga Pakistan ta hanyar Turai (Hamburg) zuwa Najeriya.
“Wadannan tramadol an boye su a bayan kwalaye na abin taje kai.

“Abdallah ya ce zai je tushen wannan binciken kuma ya umarci sauran hukumomin tsaro da su hada kai da NDLEA don cimma nasarar gudanar da binciken.

Sanarwar ta ce “ya yabawa ‘yan sanda, hukumar NAFDAC da sauran hukumomi saboda hadin kan da suke bayarwa kan wannan lamarin,”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button