Ilimi

Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire (WAEC) Ta Ce Zata Bawa Malamai Da Dalibai Kariya Daga Cutar Covi-19.

Daga Excellency Isa Hamza.

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta yammacin Africa (WAEC) reshen kasar Najeriya ta ce ta shirya tsaf wajen bayar da kariya ga Malamai da Daliba domin hana yaduwar annabar Covi-19 yayin gabatar da jarrabawar.

A kokarinsa na baiwa Dalibai da Malamai kariya, Mataimakin Gwamnan jahar Kano Dr.Nasiru Yusuf Gawuna ya tabbatar da bayar da kariya ta hanyar yin feshi a makarantun dake fadin jahar Kano.

A wani bangaren kuma, Dalibai na ta korafi saboda gwamnati ta ce za a fara jarabawar WAEC ne bayan komawar dtaliban da kwanaki biyar, inda wasu ke ganin lokacin yayi kadan, ba za su iya yin bitar darussan su ba a wadann kwanaki.

Fatanmu dai shine Allah ya bawa wandanan dalibai sa’a a jarabawoyinsu, kuma Allah ya zaunar da kasarmu lafiya dama Duniya baki daya.

Arewa Students Orientation Forum.
08148635569 ASOF

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button