Ilimi
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a JAMB Zata Zauna Dan Tattaunawa Akan Maganar Guraben Karatu A Yau.

Daga Comr Yaseer Alhassan
Hukumar dake kula da bada guraben karatu na shiga jami’o’in Najeriya, JAMB ta bayyana cewa a yau, Litinin zata zauna da masu ruwa da tsaki dan fitar da sabuwar ranar fara aikin baiwa Sabbin Dalibai guraben shiga jami’a.
JAMB a baya a irin wannan zama da ta yi ta bayyana ranar 22 ga watan Augusta a matsayin ranar da zata fara bayar da Admission.
Saidai saboda yanda gwamnati ta tsara cewa za’a yi jarabawar kammala sakandare a ranar 17 ga watan Augusta, JAMB din ta yanke shawarar dage fara aikin samarwa da dalibai Admission din saboda da yawansu da suka rubuta jarabawar basu da sakamakon kammala Sakandare a hannunsu.