Hukumar Soji Ta Yiwa Gwamnatin Jihar Borno Tonon Silili.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Bayan zargin cewa akwai kananan hukumomi 17 dake karkashin harin Boko Haram a Borno, hukumar soji ta bakin meai magama da yawunta, Sagir Musa ta karyata wannan ikirari.
Ya bayyana cewa babu wata Karamar hukuma a Borno dake karkashin Boko Haram.
Sagir yace babu wanda zai karyata cewa akwai sauran Boko Haram a Borno, amma basa rike da koda karamar hukuma 1.
Yace ya kamata mutane su tambayi dalilin da yasa yaki da Boko Haram a Borno ya sha banban da wanda ake yi a jihohin Yobe, Adamawa da sauransu.
Jaridar TheNation ta rawaito cewa Sagir yace a Borno akwai kananan hukumomin da babu titin da zai kaika garin.
Yace babu titunan da jihohi suka gina, wasu titunan tun wanda aka gina na taletale ne kuma sun lalace sai an yi zagaye sosai kafin a shiga garuruwa da dama.
Yace in banda titunan Gwamnatin Tarayya, yawanci babu titunan dake kaiwa wadannan garuruwa.
Yace ya kamata mutane su san halin da sojoji ke yaki a Borno.
Da aka tambayeshi cewa akwai wasu kananan hukumomi kusan 4 da babu kowa a ciki sai sojoji.
Yace wadannan kananan hukumomi da ake magana babu kasuwa, ba makaranta da sauran al’amuran rayuwa shiyasa mutane suka tsere, yace su kuma sojoji ai basu ne zasu samar da mutanen da zasu zauna a wadannan garuruwaba.