Labarai

Hukumar Yaki da rashawa ta fara binciken Ganduje kan batun Bidiyon sun Kuma dalar Amurka a aljihu.

Spread the love

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) na binciken tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, sakamakon yada bidiyon da ake zargin na karbar cin hanci a yanar gizo.

A wata ganawa da manema labarai shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimingado ya tabbatar da kama tsohon kwamishinan jihar Injiniya Idris Wada Saleh, wanda ake zargi da hannu a badakalar naira biliyan 1.

Dangane da takaddamar da ta dabaibaye Gwamna Ganduje, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya yi alkawarin sake bude bincike kan lamarin tsohon gwamnan. Bidiyon da ake magana a kai sun nuna yadda Ganduje ya ke karbar wasu makudan kudade na dalar Amurka, wadanda ake zargin ‘yan kwangila ne, ya kuma cusa su cikin aljihun rigar sa. Sai dai Ganduje ya musanta wadannan zarge-zargen.

Rimingado ya bayyana cewa hukumar ta fara gudanar da bincike a hukumance kuma a halin yanzu tana nazarin rahotannin bincike da suka shafi bidiyon. Duk da ikirarin da wasu mutane ke yi, hukumar ba ta samu wani umarnin kotu da ya hana su ci gaba da bincikensu ba.

Bugu da kari, Rimingado ya sanar da jama’a cewa an aike da wasika zuwa ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), inda ta bukaci hadin kan su wajen gudanar da bincike da kuma gurfanar da tsohon gwamnan. Yayin da hukumar ke jiran amsa daga EFCC, za ta ci gaba da gudanar da bincike tare da yi wa EFCC da sauran hukumomin bincike maraba idan sun zabi ba da hadin kai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button