Rahotanni

Hukumomin kasar Birtaniya sun kaddamar da shirin kwace sama da Naira biliyan 100 daga hannun tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori

Spread the love

Shugaba Tinubu Da James Ibori

Lauyan ya kuma shaida wa kotun cewa Mista Ibori na fuskantar barazanar daurin shekaru biyar zuwa 10 a gidan yari idan ya kasa biyan kudin.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumomin kasar Birtaniya sun kaddamar da shirin kwace sama da Naira biliyan 100 daga hannun tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori da ake tuhuma da karkatar da kudade.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, Jonathan Kinnear, babban mai shigar da kara na jihar, ya shaida wa kotun a ranar Alhamis cewa adadin kudaden da ya kamata a kwace daga hannun Mista Ibori ya kai fam miliyan 101.5.

Lauyan ya kuma shaida wa kotun cewa Mista Ibori na fuskantar barazanar daurin shekaru biyar zuwa 10 a gidan yari idan ya kasa biyan kudin.

Kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa ya ba da rahoton cewa alkali a Kotun Southwark Crown, David Tomlinson, ya yi “binciken gaskiya” game da kudaden kuma ana sa ran zai ba da oda a ranar Juma’a ko kuma jim kadan bayan haka.

Hukuncin da alkalin ya yanke zai kawo karshen cece-kucen shari’a na tsawon shekaru goma kan yunkurin kwace kadarorin.

Wannan dai na zuwa ne bayan shekaru bakwai da tsohon gwamnan ya dawo Najeriya bayan hukuncin daurin da aka yanke masa a gidan yari bisa samunsa da laifin karkatar da kudade.

Shi dai Mista Ibori mai shekaru 63 a duniya, tun bayan da aka sako shi daga gidan yari a kasar Birtaniya, ya ci gaba da nuna halin ko-in-kula, inda ya mayar da hankalinsa a siyasa kawai kan jihar Delta mai arzikin man fetur, har sai da ya fito fili bayan ganawarsa da shugaban kasa Bola Tinubu, wanda ya tarbe shi har sau biyu a fadar shugaban kasa ta Villa dake Abuja, tare da wasu tsoffin gwamnoni.

A shekarar 2011, an tasa keyar Mista Ibori daga Dubai zuwa Landan, kuma an tuhume shi da laifin yin almundahana da “karkatar dukiyar da aka samu.”

Ya amsa laifuffuka goma da suka hada da zamba da karkatar da kudade a shekarar 2012, sannan kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari, wanda Birtaniyya ta yi la’akari da shi a matsayin wani lamari mai cike da rudani a yaki da cin hanci da rashawa.

A gefe guda kuma hukumomin Burtaniya sun yi alkawarin mayar da duk wani kudaden da aka karba daga hannun Mista Ibori zuwa Najeriya. Ta kwato Fam miliyan 4.2 da aka kwace daga hannun tsohuwar matar Mista Ibori da kuma ‘yar uwarta, wadanda kuma aka tura gidan yari saboda taimaka masa wajen karkatar da kudade a shekarar 2021.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button