Lafiya

Hukumuar Kula Da Ingancin Abinci Da Magunguna Ta Amurka FDA Ta Bayar Da Umarnin Fara Amfani Da Kwayar Remdesivir A Matsayin Maganin Cutar Korona, A cetwar Shugaba Donald Trump.

Spread the love

Daga Abdul Aziz Muhammad

Trump ya ce shugaban kamfanin Gilead, wanda ya samar da kwayar, ya bayyana yunkurin a matsayin mai matukar amfani kuma irinsa na farko, sannan zai bayar da kyautar kwalabar allurar miliyan daya.

Mataimakin Trump, Mike Pence ya ce za a fara raba maganin zuwa asibitoci a ranar Litinin.

Maganin wanda tun farko aka samar domin magance cutar Ebola, na rage yawan alamun cutar daga 15 zuwa 11 a wani gwaji da Amurka ta yi a asibitoci a fadin duniya.

Kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Masar da Tanzania da Afirka ta Kudu, su ma suna kan yin gwajin wasu magungunan cutar, a cewar hukumar Africa CDC mai yaki da cutuka masu yaduwa a Afirka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button