Hukuncin kotun korafin zabe na Kano fyade ga tsarin Dimokuradiyya ~Cewae Kungiya
Wata kungiya da aka fi sani da Coalition For Democratic Rights ta bayyana rashin jin dadin ta kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano ta yanke na korar gwamnan jihar Yusuf Abba na jam’iyyar New Nigeria People’s Party tare da bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Nasir Gawuna a matsayin. wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, yana mai cewa hukuncin fyade ne a kan ka’idojin tsarin dimokradiyyar Najeriya.
Kungiyar a cikin wata sanarwar manema labarai da Daraktan yada labarai na ta Ibrahim Babayo, ya fitar, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki, bangaren shari’a, hukumar zabe, jam’iyyun siyasa, da sauran jama’a da su fito da kyakkyawan tsarin gaskiya, adalci da bin doka da oda. wajen sauke nauyin da tsarin mulki ya dora musu.
ba son zuciya ba.