Ibrahim Magu Ya Nemi Kwamiti Bincike Ya Rufa Masa Asiri Kan Zargin Da Ake Yi Masa Saboda Shi Maraya Ne.
Tshon Shugaban Rikon kwarya Na Hukumar Nan Mai yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu, ya Roki Kwamitin Nan da Mai Shara’a Ayo Salami, ke Jagoranta da ya Rufa masa Asiri kan Zargin da ake masa Na Cin Amanar Hukumarsa Ta EFCC, Lokacin da yake Jagorantar Hukumar.
Magu, ya gabarda bukar tasa ne, Lokacin da aka gayyato shi Gaban Kwamitin domin Jin Bahasinsa aka Wasu Jiragen Ruwa da Hukumar Sojan Ruwa ta Kamo ta Mikasu ga EFCC lokacin da magu ke jan ragamar Hukumar, bayan An mika jigen ruwan ga EFCC an tabbatar da Na Laifine amma Magu ya Saki Jiragen aka wuce dasu.
Kwamitin da ta tuntubi Magu, meyasa ya saki Jiragen Sai Magu yace Baisan da maganar ba, amma da Hukumar Sojin Ruwa ta kawo Shedan yin Haka a Rubuce Magu ya kasa cewa komai, Sai yace Wannan Kwamiti dake wannan Bincike ta Rufa masa Asiri Shi Maraya ne.
Magu yace “Tunda Iyaye Na suka rasu Na rasa masu bani shawara shi yasa nayi Ire-iren wannan Kuskuren lokacinda nake Jagorantar Hukumar.
Ko a Kwanakin baya Kwamitin Na Ayo Salami, ya bankado manya manyan Laifuka da Ibrahim Magu, ya aikata a Hukumar, kama daga;- Kashe muraba da Barayin gwamnati, Karbar Nagoro hannun barayi, Kwato biliyoyin kudi da gidaje daga barayin gwamnati ya halattawa kansa.
An kamashi da hada kai da wani limamin coci, Pastor Emanuel Omale, yana Karbar Na goro hannun Barayin gwamnati yana Ajiye Masa, an kama shi da laifin hada kai da Masu chanjin kudin kasar Waje Na Kan Fanin Shanono dake Kaduna, Suna karbar Rashawa daga barayin Gwamnati suna Ajiyewa Magu domin Badda Bami.
Duk wadanda ake zargi da hakan An gayyacesu An Gayyaci Magun gaban Kwamitin kuma an Tabbatar da Laifin da ake zargin Magun.
Masu karatu Idan Baku mantaba Tun a lokacin da aka Mika Sunan Ibrahim Magu, Zauren Majalisa a shekarar 2015, domin Tabbatar dashi a matsayin Wanda zai jagoranci Hukumar ta EFCC, a Lokacin Bukola Saraki, ne Shugaban Majalisar, Hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun Rubuto Takadda gaban Majalisar domin kar a yadda a Amince da Magu a Wannan Hukumar domin tun a baya an samu Magu da Cin Hanci da Rashawa da Cin Amanar Kasa.
Dalilin haka Majalisar taki amincewa dashi, Sai Gwamnati ta Maida abin Siyasa ta bashi Rikon Kwarya a Hukumar Har Na tsawon Shekaru Biyar.
Sai yanzu da wannan ta Taso ake Ganin Abinda DSS da Saraki Sukayi Sunyi kwazo amma Gwamnati ta siyasantar da abin Yanzu gashi nan Yayiwa Tattalin Arzikin Kasa Illa.
Duk Dan Najeriya yanzu Ya sanya Ido ne, Yaga Wanne Irin Hukunci Za’a yiwa Wannan Mutumin da ya tafka Cin Hanci da Rashawa a Hukumar, EFCC da sunan EFCC a Gwamnatin da tace Zatayi yaki da Cin Hanci da Rashawa babu ji ba Gani.
Akwai Sauran Labirin Na Nan Tafe.
Daga Shafin:- Ahmed T. Adam Bagas