Idan Ana Son Kawo karshen Boko Haram Sai Buhari Ya Cire Burtai~ Sergeant Omorege.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
A yau Alhamis ne Wani Tsohon Sojan Nigeria Mai Mukamin Sergeant Omorege Da ya yiwa Jaridar Sahara Reforters Karin Haske yace Idan Har dagaske ake so akawo karshen Yan Ta’addan Boko Haram da suka Addabi Arewa maso Gabashi Kasar nan, To yazama Wajibi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Sallami Hafsan Hafsoshin Nigeria Gen. T.Y Burtai da Gidan Soja.
Kuma Idan Baku mantaba Watannin baya wasu Manyan Kasar Nan wasu Kungiyoyi sun Shawarci Shugaba Buhari da ya sallami Burtai din ko za’asamu Cigaba a sashin Tsaro amma Shugaban Yayi Biris da Wannan Shawarwarin.
Sergeant din yayi Wannan Bayanin ne bayan Yan Boko Haram din sunkaiwa Gen. Burtai Hari yau a Sansanin da yake a Ngamdu Na Jahar Borno dake Arewa maso Gabashin Kasar Nan.
Masu karatu Ko Kuna goyon bayan Shawaran da Sergeant din ya baiwa Buhari…???