Idan Buhari ya bani dama Zan iya dawowa da Nageriya dala Bilyan $10bn Cikin kwana 30 ~Maina
Tsohon Shugaban Kwamitin Gyaran Fansho, PRTT, Abdulrasheed Maina, ya bayyana cewa zai iya dawo da kasar Nageriya da dala biliyan 10 na fansho da aka sace a cikin kwanaki 30 idan Shugaba Muhammadu Buhari ya ba shi dama.
Mista Maina ya yi wannan bayanin ne ta bakin mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Aliyu Musa, a jihar Kaduna, don bikin cikar shekaru 60 da samun ‘yancin kai A cewarsa, irin wadannan kudaden na iya taimakawa wajen gyara gibin kayayyakin more rayuwa, tallafin mai da kuma inganta kudin wutar lantarki wanda a karshe zai sanya masana’antar ta ci gaba matakin da ma’aikatan Najeriya suka tsayar.
“Maina ya nuna cewa, a shirye yake sa zaran ya murmure daga aikin da aka yi masa a makon da ya gabata. “Tsohon dan Fensho din ya ci gaba da nuna cewa, zai iya dawo da wadannan kudaden ne kai tsaye ga Shugaba Buhari, yayin da ya nuna tsoron cewa, za a iya sake wawure kudin idan ba a sarrafa ta yadda ya kamata. Mista Maina ya ce
Maina ya taimaka wa gwamnatoci musamman na Tsohon Shugaba Jonathan inda ya dawo da Naira tiriliyan 1.6 da kuma a cikin gwamnatin Shugaba Buhari, inda ya dawo da Naira tiriliyan 1.3.3 da wasu kadarorin