Idan Da Rai Da Rabo Wai Kuturu Ya Hangi Baturiya.

Daga Mutawakkil Gambo Doko
Ƙasar Singapore ita ce ƙasa ta uku ta fuskar tattalin arziƙi a duniya, sannan ta 19 a girma , tana da adadin mutane million 5.6. Bugu da ƙari, Babban filin saukar jiragen sama na ƙasar Singapore mai suna Chanji Airport shine mafi kyau a faɗin duniya. A hannu ɗaya, Ƙasar Singapore ita ce ta biyar a jerin ƙasashen da suka fi tsafta a duniya.
√ A ƙasar Singapore haramun ne siyar ko siyen chewing gam saidai a kantin siyar da magunguna mai lasisi. Sannan bayan sun siyar maka sai sun rubuta sunanka. Wannan haramcin ya samo asali ne tun ranar 3 Jan 1992 a loƙacin mulkin tsohon firayiministansu mai suna Lee Kuan Yew. kuma duk wanda aka kama yana siyar da ita za’a cishi tara ko zaman gidan yari na shekara biyu . Sannan haramun ne shigo da Chewing gam ƙasar saidai ta ɓarauniyar hanya, dan haka al’ummar suke shiga maƙwobtan ƙasashe domin siyanta.
√ A ƙasar Singapore idan mutum yayi amfani da banɗaki bai wankeshi ba da ruwa sai an ci tararsa
√ A ƙasar Singapore idan ka kunna kiɗa wanda zai takurawa jama’a sai an ci tararka. Da sauransu
*MENENE SIRRIN CIGABAN ƘASAR SINGAPORE
A Baya, Ƙasar Singapore ta kasance ƙasa ce marar ƙarfin tattalin arziƙin ƙasa , ga jahilci da ƙazanta har izuwa mulkin Firayaministan ƙasar #Lee Kuan Yew# wanda ya kashe shekaru 30 yana mulkin ƙasar, cikin ƙanƙanin loƙaci tattalin arziƙinta ya ginu ta koma kyakykyawar ƙasa.
Dan haka watarana ake yi masa tambaya menene sirrin daya saka loƙaci guda ya chanja ƙasar Singapore, Shine yake bada amsa da cewa maimaikon ya karkartar da kasafin kuɗin ƙasar a fannin siyo makaman yaƙi da harkar tsaro, sai ya karkatar da mafi yawan kasafin kuɗin ƙasar ga fannin ilmi. Dan haka , a taƙaice zamu iya cewa baiwa ilmi fifiko da shugaba Lee Kuan Yew yayi shine sirrin cigaban ƙasar Singapore.
*DARASI
A yau matsalolin da suke addabar Najeriya musamman yankinmu na Arewa idan zamu cire son zuciya, hassada ,munafurci mu kinsa cigaban ƙasarmu ko yankinmu a cikin zuƙatanmu sannan shugabanninmu suyi koyi da firayiministan Singapore Lee Kuan Yew ta fuskar baiwa fannin ilmi fifiko tare da shimfiɗa mulkin adalci da ƙasarmu ta kai matsayin da bama tsammani. Amma babbar matsalar ita ce kowa ya bada kai bori ya hau akan Najeriya ko Arewa basu gyaru ba. Wanda babban sinadarin nasara a rayuwa da farko shine samun cikakken yaƙini akan abin daka saka a gaba.