Idan Kun Isa kuzo ku rantse da Alkur’ani cewa baku saci ku’din talakawan jihar Kaduna ba El rufa’i ya fa’dawa tsoffin gwamnonin jihar Kaduna.
Gwamna Nasir Ahmad El-Rufa’i na jihar Kaduna ya kalubalanci tsaffin gwamnonin jihar da su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su saci dukiyar al’umma ba don gina gidaje a jihar da kuma Dubai.
Ya jefa kalubalen ne a tattaunawar sa ta kafafen yada labarai ta Sashen Hausa na Hukumar Yada Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC).
A cewar El-Rufa’i, daya daga cikin tsofaffin Gwamnonin ya gina wani katafaren gida a kan titin Jabi, Kaduna GRA bisa zargin sata.
A bar Gwamnonin da suka shude su fuskanci al’ummar Jihar Kaduna su rantse da Alkur’ani mai girma cewa ba su taba sata a asusun gwamnati ba. Zan iya rantse ban taba satar Kobo a asusun gwamnati ba.
Na yi farin ciki da abin da muka gani. Ayyukan da muka fara da ingancin ayyukan, za mu kwashe shekaru muna jin dadin su.” Inji shi.