Ikirarin Karya Na Obadiah Ya Tabbatar Da Gargadin Da Muka Yi Cewa Wasu Nason Tarwatsa Kasarnan DSS
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS ta bayyana cewa ikirarin karya na tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, CBN, Obadiah Mailafiya na cewa kwai gwamna Kwamandan ‘yan Boko Haram ya tabbatar da gargadin da suka yi na cewa wasu manyan mutane na kokarin tada fitina a Najeriya.
DSS ta bayyana cewa bayan da suka gayyaci Mailafiya ofishinsu a Jos, cikin rawar jiki ya bayyana cewa, a yi hakuri kan kalaman nasa.
Tace a matsayinshi na tsohon shugaba a CBN da kuma mukamin da yake rike dashi yanzu, yasan yanda ake kaiwa hukumomi irin wannan rahoto amma duk da haka ya zabi ya gayawa Duniya dan kawai cimma wata Manufa.
DSS tace tana gargadin duk wani ko kuma wata kungiya masu irin wannan manufa ta tunzura jama’a su kiyaye dan ba zata yi kasa a gwiwa wajan kama duk wanda ya taka dokar kasa ba.
Kaman Yanda Muka ruwaito muku cewa DSS ta bukaci ‘yan kasa su ci gaba da gudanar da al’amuransu kamar koda yaushe dan suna aiki tukuru wajan samar da tsaro.