Ilimi

ASUU: Malamai 10 sun mutu tun bayan fara yajin aikin – UNICAL

Spread the love

Kungiyar malaman jami’o’i reshen Calabar, ta bayyana cewa goma daga cikin ma’aikatanta sun mutu tun bayan fara yajin aikin ASUU a ranar 14 ga Fabrairu, 2022.

Shugaban kungiyar ASUU UNICAL reshen, Dr John Edor ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin da yake zantawa da Jaridar PUNCH a Calabar.

Ko da yake, Edor bai bayyana halin da ake ciki na mutuwar malaman ba, amma wasu na zargin rashin kudi da za a bi domin kula da lafiyarsu, a matsayin musabbabin mutuwarsu.

Dokta Edor, ya bayyana sunayen malaman da kwasa-kwasan da suke koyarwa.

Sunayen da aka lissafa sune; Farfesa E. O. Udosen, Biochemistry; Dr. Mrs. Iquo Takon, Microbiology; Farfesa G. U. Ntamu, Nazarin Addini da Al’adu; Farfesa Misis Judith Otu, Ilimin zamantakewa; Farfesa Victor Ibianwu, Physics, Farfesa Offiong Abia, Tarihi da Nazarin Duniya; Farfesa Catherine Agbor, Ilimin Fasaha; Dokta Augustine Bassey, Ilimin zamantakewa; Dokta Ita Esuabana, Lissafi da Dokta Chinyere Okam, Gidan wasan kwaikwayo da Nazarin Media.

ASUU ta fara yajin aikin ne domin matsawa bukatar su na samun walwala, da dai sauran su kuma gwamnatin tarayya ta hana albashin malaman na tsawon wata bakwai.

Da aka nemi ya yi tsokaci game da bala’in, Edor ya ce, “Ba zan kara yin tsokaci ba.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button