Ilimi

Bayan Ciyar Da Dalibai, Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Tsutsar Ciki Na Daliban Najeriya Miliyan Guda

Spread the love

Daga Comr Abba Sani Pantami

Ma’aikatar tallafi da jin kai ta bayyana cewa zata baiwa daliban makarantun firamare guda milyan daya maganin kashe tsutsar ciki don inganta lafiyarsu.

Shugaban shirin NSIP, Dr Umar Bindir, ya bayyana hakan a zaman shirye-shirye na tsawon kwana biyar dake gudana a birnin tarayya Abuja ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai NAN yace daya daga cikin manufofin zaman shine samar da kayayyakin kashe tsutsar cikin dalibai.

Mr Bindir, wanda ya samu wakilcin mataimakiyar diraktar shirye-shirye, bincike da lissafe-lissafe a ma’aikatar, Safiya Sani, ya bayyana muhimmancin kashe tsutsar cikin don inganta lafiyansu.

Daga Comr Abba Sani Pantami

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button