Ilimi
DA DUMI-DUMI: Nan da ‘yan kwanaki za a janye yajin aikin ASUU – Falana

Babban Lauyan Najeriya, Femi Falana ya bayyana fatansa cewa za a janye yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta fara a kwanaki ba makonni ba.
Babban Lauyan ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da littafin mai suna Breaking Coconut With Your Head, na Lanre Arogundade ranar Litinin a Legas.
Ya bayyana cewa akwai yiwuwar a kammala yajin aikin a wajen kotun.