Dan Talaka Ya shirya Biyan makudan Kudade a Jami’o’in Nigeria-Dr. Almuhajir

Dole Ya’yan Talaka Su shirya Biyan Makudan Kudade a Jami’a.

Yanzu dai a takaice gomnati na nufin cewa dole ya’yan talaka da suke karatu a jami’o’in kasar nan su shirya domin su biya makudan kudaden karatu.

Saboda bayan zaftare albashin Malamai, sabon tsarin IPPIS ya cire kudaden da ake biyan Casual staff da suke cike guraben Malaman da babu su, kwararrun Malamai da ake dauka saboda kwarewa on contract, part time professionals, external assessment, external examinationare sannan an cire kudaden da ake tafiyar da tsangayoyi da sashe-sashe na ilimi wadanda idan babu su babu Jamiah.

Babu kudaden Seminar Departmental da faculty, babu na escortions and field operations da sauran abubuwa da yawa da ba za su kirgu ba.

Kun ga yanzu burin wadanda suke ganin kamar Malaman suna fada da IPPIS saboda kashin kan su be zasu yi tarayya da Malaman wajen dandana kudar su, domin dole su biyan kudin wadannan abubuwa tunda gomnatin ta yi nasarar fidda su daga jadawalin ta.

Dr. Sheriff Almuhajir yayi wannan tsokacin ne a shafin sa Na Facebook.

Leave a Reply

Your email address will not be published.