Ilimi

Don kawo karshen rashin tsaro dole ne gwamnati ta saka hannun jari a fannin ilimi maimakon gadar sama – Gumi

Spread the love

Ahmad Gumi, malamin addinin Islama, ya ce domin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya, dole ne gwamnati ta saka hannun jari a fannin ilimi maimakon aiwatar da “ayyukan gadar sama”.

Malamin addinin Musuluncin ya ce rashin tsaro a Najeriya “mai hawa uku ne, na talauci da jahilci da rashin adalci”.

A wata hira da Sunday Sun, Gumi ya ce dole ne gwamnati ta sake tunani a kan bukatar samar da kayan aiki ga wadanda ke karkashin kasa da kuma saka hannun jari a iliminsu.

Malamin addinin Musuluncin ya ce, idan ba a bawa ‘yan kasa ilimi ba, matsalar tsaro za ta ci gaba da wanzuwa saboda jahilci da rashin aikin yi ne ke haddasa shi, wadanda ke haifar da rashin samun ilimi.

“Almajirci wani tsari ne na ilimi wanda ya dade, kamar yadda ake amfani da jakuna da rakuma a matsayin hanyar sufuri ta da wanda a yanzu tsarin sufuri na zamani ya mamaye shi.

“Don haka, idan ka samar da na zamani, mutane za su bar na da. Bari in ce watakila har yanzu muna da ƙauyuka inda har yanzu suna amfani da jakuna da raƙuma suna yawo.

“Idan ka duba, za ka gane cewa babu hanyoyi masu kyau, balle ma motoci masu kyau a irin wadannan wuraren. Don haka, Almajarai ba makaranta ba ce kawai, a’a tsarin ilimi ne wanda ba shi da isasshen kuɗi.

“Yaro bayan ya dauki darasin safe, zai je ya nemi abinci domin abincin nan yana ciyar da kanshi ya baiwa mallam kadan.

“Don haka dole ne mu mai da ilimi tun daga firamare zuwa sakandare har ma da manyan makarantu ya zama abin duniya.

“Ku kashe kudi a fannin ilimi maimakon gadar sama domin rashin tsaro nau’i uku ne, na talauci, jahilci da rashin adalci. Don haka zabar dubunnan yara daga cikin miliyoyin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya tamkar digo ne a cikin tekun matsalar da muke fama da ita.

“Ci gaban na iya baiwa wasu Almajarai kwarin guiwa su fara zuwa cikin gari don gwada sa’ar su a kan tallafin karatu da alawus. Ayi wata manufa inda ilimin firamare zai zama cikakkiyar kyauta tare da sanya tsarin dorewa a wurin.

“Kamar yadda Awolowo ya yi a tsohon yankin yamma. Na tuna a wancan lokacin shi ne “ilimi kyauta” kuma wannan shi ne abin da muke bukata domin idan ba ku ilimantar da jama’a ba, matsalar za ta ci gaba da tafiya domin kashi daya bisa uku na cututtukan da kuke gani a kusa suna haifar da jahilci da rashin aikin yi, wadanda ke da dangantaka kai tsaye da ilimi.

“Idan ba ku koya wa mutane dabarun da ake buƙata don yin aiki ta hanyar ilimi ba, ta yaya za su tsira ko da kuna ba su alawus kowane wata? Don haka ya kamata gwamnati ta sake tunani, ta rage duk wadannan ayyuka na giwaye, sannan ta samar da kayan aiki tun daga tushe domin tabbatar da cewa kowane dan Najeriya ya samu ilimi.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button