Hukumar JAMB Ta Zargi Jami’ar Abuja Da Bada Guraben Karatu Ba Bisa Ƙa’ida Ba.

Hadaddiyar Hukumar Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta sanya Jami’ar Abuja (UniAbuja) a cikin cibiyoyin da ke gudanar da bada guraben shiga ba bisa ka’ida ba.

A wata sanarwa, Shugaban, Hulda da Jama’a na JAMB, Fabian Benjamin a ranar 13 ga watan Afrilu, ya ce jami’ar na daga cikin cibiyoyin da ke ba da guraben shiga ga dalibai ba tare da sanin hukumar ba.
Ya ce: “Sakamakon haka, irin wadannan guraben shiga sun saba doka, ba za a karbesu ba kuma ya saba wa dokoki da ka’idoji da ke jagorantar shiga manyan makarantu a Najeriya kamar yadda Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta amince kuma aka bayar a CAPS.”

Bugu da kari, kakakin na JAMB, kamar yadda TheCable ta ruwaito, ya ce jami’ar ta kuma bukaci dalibai su biya kudin karbar guraben shigar.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *