Kaso 75% na ɗaliban jami’ar “Kaduna State University (KASU)” ka iya rasa guraben karatun su sakamakon ƙarin kuɗin makaranta ~ ASUU

Ƙungiyar jami’o’i ta ƙasa (ASUU) reshen Jami’ar Kaduna State University (KASU) ta bayyana cewa aƙalla kaso 75% na daliban makarantar ka iya rasa guraben karatunsu sakamakon ƙarin kuɗin makarantar da ake shirin yi.

Ɗaya daga cikin shuwagananni a makarantar mai suna Peter Adamu shine ya bayyana hakan a wani jawabi na musamman; ya bayyana cewa mafi akasarin ɗaliban ka iya barin makarantar saboda iyayen su, ba su da ƙarfin ɗaukar nauyin biyan irin waɗannan makudan kuɗaɗe da ake shirin ƙarawa.

Mista Peter Adamu ya ƙara da roƙon gwamnatin Jihar Kaduna da ta ƙara yin duba na tsanaki bisa ga ƙudurin ƙara kuɗin makarantar. A cewarsa, ilimi dama ce, bawai gata ba, kuma tallafawa ɓangaren ilimi kamar yadda kundin tsarin mulki na ƙasa ya tanada alhaki ne na gwabnati ba iyayen ɗalibai kaɗai ba.

Makarantar ta “Kaduna State University (KASU)” tana da aƙalla ɗalibai dubu 19 wanda kuma sama da mutum dubu 17 yan asalin Jihar ta Kaduna ne.

Ya ƙara da cewa; kaso saba’in na ɗaliban da suke karatu a makarantar ƴaƴan talakawa ne, waɗanda suka haɗa manoma da ƙananan ƴan kasuwa. Hakazalika baya ga yadda kwana-kwanan nan gwamnati ta sallami wasu daga cikin iyayen wadannan yara daga aiki, yanzu kuma a bijiro da wannan kudiri, Peter Adamu ya nuna takaicinsa.

Har’ilayau; ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici yadda gwabnati batayi duba da irin yadda anguwanni da tituna suka zama hatsari sakamakon ta’addanci, dabanci da kuma ayyukan masu garkuwa da mutane ba; wanda a ƙarshe ya bayyana rashin samun ingantaccen ilimi da aikin yi a matsayin silar waɗannan fituntun da ake fuskanta. “Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta bayyana.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *