Kotu Ta umarci ASUU da ta janye yajin aiki

Kotun kolin masana’antu ta kasa ta umarci kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), da ta dakatar da yajin aikin da take yi.

Da yake yanke hukunci a kan umarnin shiga tsakanin da gwamnatin tarayya ta shigar, Mai shari’a Polycarp Hamman ya hana ASUU ci gaba da yajin aikin har sai an yanke hukunci.

Mai shari’a Hamman wanda alkali ne na hutu ya bayar da umarnin a mayar da karar da aka shigar ga shugaban kotun masana’antu domin a mayar da shi ga wani alkali.

Alkalin ya ci gaba da cewa matakin na masana’antu na da illa ga daliban jami’o’in gwamnati wadanda ba za su iya samun damar halartar manyan makarantu masu zaman kansu ba.

Ya ce dokar takaddamar kasuwanci ta umurci ma’aikata da kada su shiga yajin aikin da zarar an mika wata matsala ga kotun masana’antu.

Mai shari’a Hamman ya kuma amince da bukatar gwamnatin tarayya inda ya ce ya dace kuma an amince da shi.

Don haka kotun ta hana ASUU, ko su kansu, mambobin kungiyar, wakilai, masu zaman kansu ko kuma duk wanda aka kira, daga daukar wasu matakai da kuma yin duk wani mataki na ci gaba da yajin aikin har sai an saurari karar da aka shigar.

Alkalin ya ki ci tarar gwamnatin tarayya kamar yadda kungiyar ASUU ta bukata.

Wannan odar na zuwa ne sa’o’i kadan bayan kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta yi barazanar cewa ba za ta bari a gudanar da wani gangamin siyasa a fadin kasar ba har sai daliban jami’o’in gwamnati su koma azuzuwa.

Shugaban kungiyar NANS na kasa Ojo Olumide ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a ranar Laraba, wasu kwanaki har zuwa ranar 28 ga watan Satumba, ranar da ‘yan takara za su fara yakin neman zabe kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanar. .

“Toshewar hanyoyin da jama’a ke bi da tashoshin jiragen ruwa, gargadi ne kawai. Idan har gwamnati ta gaza kammala duk wata tattaunawa da sulhu da ASUU a cikin wa’adin makonni biyu, to za su kara fitowa zanga-zanga da gangami a duk fadin kasar nan, za su kuma shaida bacin rai, da takaicin daliban Najeriya da suka kasance a gida watanni bakwai da suka gabata.

“Kamar yadda muka yi masu alkawari ba za mu bari a gudanar da wani gangamin siyasa a fadin kasar nan ba har sai mun dawo aji. Wannan gwamnati ta jefa daliban Najeriya da dama cikin damuwa. Sai mu ce ya isa; ba za mu sake jure wa wannan rikici da za a iya kaucewa a cikin al’ummar mu ba a hasumiya ta hauren giwa,” inji shi.

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 sakamakon tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya da malaman jami’o’in gwamnati ba ta kai ga cimma matsayar da dalibai za su iya komawa aji ba.

A kokarin da gwamnatin tarayya ta yi na dawo da malaman makarantar boko, gwamnatin tarayya ta kai kungiyar ASUU gaban kotun masana’antu ta kasa.

A wata sanarwa da shugaban ‘yan jaridu da hulda da jama’a na ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, Olajide Oshundun ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya ta dauki matakin ne bayan tattaunawar da aka yi tsakaninta da ASUU.

A cewarsa, gwamnati na son kotun masana’antu ta kasa ta umarci ‘yan kungiyar ASUU da su koma bakin aiki, yayin da kotun ke fuskantar matsalolin da ake ta takaddama a kai.

Takardar magatakardar kotun masana’antu ta kasance mai kwanan wata 8 ga Satumba, 2022, kuma Ministan Kwadago da Aiki, Sanata Chris Ngige ya sanya wa hannu.

A martanin da ta mayar kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na shari’a, ASUU ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan tilastawa mambobin kungiyar da ke yajin aiki komawa aji ta hanyar umarnin kotu.

A cewar shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, kawai mutum zai yi mamakin irin koyarwar da ma’aikatan ilimi za su yi bayan an tilasta musu komawa ajujuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *