Ilimi

Kotun ɗaukaka ƙara ta umurci ASUU da ta janye yajin aiki nan take

Spread the love

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja, ta umarci mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su koma bakin aiki ba tare da bata lokaci ba.

Kotun daukaka kara ta bayar da wannan umarni ne a wani hukunci da ta yanke kan bukatar da kungiyar ta ASUU ta yi na neman a ba ta izinin daukaka kara kan umarnin kotun masana’antu ta kasa wadda ta bukaci malaman da ke yajin aiki su koma bakin aiki.

Kotun ta kuma bayar da izinin daukaka kara kan umarnin kotun masana’antu, tare da jaddada cewa ASUU ta bi umurnin karamar kotu daga yau 7 ga watan Oktoba.

Kwamitin mutum 3 da mai shari’a Hamman Barka ya jagoranta, ya ce ASUU ta gabatar da sanarwar daukaka kara a cikin kwanaki 7, dole ne ta nuna shaidar cewa mambobinta sun koma bakin aiki nan take.

Kwamitin ya ce rashin bin umarnin, zai sa karar ta gaza a gaban kotun daukaka kara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button