Ilimi
Ku daina kiran Pantami da suna, Furofesa. ~ASUU ta gargaɗi makarantu

Daga | Ya’u Sule Tariwa
Ƙungiyar jami’o’i ta ƙasa ASUU, ta ƙaryata zancen cewa Pantami ya samu karramawar Furofesa daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Owerri tare da umartar makarantu su daina kiransa da suna Farfesa.
Shugaban ƙungiyar ta ASUU, mai suna Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyanawa manema labaru cewa, matsayin Farfesa da aka baiwa Pantami haramtacce ne saboda bai cancanta ba.
Pantami yana daga cikin mutane bakwai da Jami’ar Ƙimiyya da Fasaha ta Owerri ta karrama da matsayin Furofesa tun a watan Satumba ta shekarar da ta gabata, lamarin da haryanzu yake cigaba da jawo cece-kuce.

