Ilimi

Kwalejin Aikin Jinya Da Unguzoma Ta Jihar Kano Za Ta buɗe Shafin Ɗaukar Ɗalibai A Gobe (Alhamis)

Spread the love

‘Kano State College Of Nursing Sciences & Midwifery’, ta shirya buɗe shafin ta, domin bawa ɗaliban da ke da sha’awar samun guraben karatu, a rassan makarantar da ke Kano da Madobi, a kakar karatu ta 2022/2023 damar cikewa.

Za a buɗe shafin ne, a gobe Alhamis, 20 ga watan Oktoba, inda kuma ake sa ran rufewa, a ranar 23 ga watan na Oktoba (kwanaki uku kacal).

WAJIBI NE, DUKKANNIN ƊALIBIN DA ZAI CIKE WANNAN FORM, YA KASANCE YA MALLAKI CREDITS, A DARUSSAN, TURANCI, LISSAFI, BIOLOGY, CHEMISTRY, DA KUMA DARASIN PHYSICS, A JARRABAWAR SA TA KAMMALA MAKARANTAR SAKANDIRE (NECO/WAEC) A ZAMAN DA BAI WUCE GUDA BIYU BA (TWO SITTINGS), SAI KUMA ONE SITTING GA ƊALIBAN DA ZA SU YI AMFANI DA NABTEB.

Yadda Ake Cikewa :

•Ɗalibi zai halarci adireshin :

https://moh.knstate.healthcare

•Bayan shafin ya buɗe, sai ya danna wurin da aka rubuta ”Apply”.

•Daga nan, sai ya sanya Email ɗinsa (ya tabbatar yana aiki), sai kuma ya taɓa maɓullin ”Submit”.

•Sai ɗalibi ya wuce cikin Inbox ko Spam ɗin Email ɗinsa, sannan ya danna link ɗin da zai ga an aike masa, domin yin verify na Email ɗin.

•Daga nan, sai ya koma, shafin, ya sanya bayanan sa, da suka haɗar da; Suna, Lambar waya, Makarantar da ya ke son cikewa, Kwas ɗin da ya ke so, da kuma Password.

•Bayan haka, sai ya cire Invoice na biyan kuɗi.

•Sai ya garzaya bankin Polaris mafi kusa da shi, domin biyan adadin kuɗin da ya gani, a jikin Invoice ɗin.

•Bayan ya biya, sai ya koma shafin :

https://moh.knstate.healthcare/application/login

•Sai ya sanya Email ɗin da ya yi rijista da shi a ɗazu, domin cigaba.

•Sai ya yi Uploading na shaidar biyan kuɗin, sannan ya ƙarasa rijistar sa.

•A ƙarshe, sai ya cire, Acknowledgement Slip ɗin sa, ya kuma jira rana, lokaci, da wurin da zai rubuta Entrance Exam, wanda zai gani bayan wani lokaci, a wannan shafin nasa.

KUƊIN APPLICATION FORM ƊIN, NAIRA 5,000 NE.

Rubutawar ✍️ : Miftahu Ahmad Panda.

Daukar Nauyi: Arewa Students Orientation Forum Da Tallafin Jaridar Mikiya

  08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button