Ilimi

Maganar Yajin Aikin ASUU Yana min Ciwo a zuciya ta ~Cewar Shugaba Buhari.

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake yin kira ga kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU da ke yajin aiki da su koma ajujuwa tare da ba su tabbacin magance matsalolin da suke fama da su ta hanyar karancin kayan aiki.

Shugaban, wanda ya sake nanata kiran a wani jawabi da ya yi a fadin kasar a ranar Asabar a Abuja, ya ce ya ji takaicin yadda ake ci gaba da tabarbarewar harkokin ilimin manyan makarantun kasar nan.

Wannan Yana kunshe ne a wani bangare ne na ayyukan bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai na kasar.

A cewarsa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da hada-hadar albarkatun kasa wajen samar da tallafin ilimi domin tabbatar da cewa ‘yan kasa sun samu ilimi da kwarewa a sana’o’i daban-daban.

“Dole ne in furta cewa ina jin zafi sosai game da tarzoma da ake ta fama da ita a tsarin karatunmu na manyan makarantu.

“Ina amfani da wannan bukin ranar samun ‘yancin kai ne domin nanata kirana ga kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke yajin aikin da su dawo ajujuwa tare da ba su tabbacin shawo kan matsalolin da suke fuskanta ta hanyar karancin kayan aiki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button