Malaman Makaranta 5,664 Za Su Kai Gwamnatin Jihar Abia Kotu.

Wasu malaman makaranta 5,664 da gwamnatin Jihar Abia ta sallama daga aiki sun yi barazanar gurfanar da ita gaban kotu idan ba a dawo da su bakin aiki ba.

A ranar Laraba lauyoyin malaman suka rubuta wa hukumar ilimin sakandare ta jihar wasiƙa suna bayyana aniyarsu ta shigar da ƙara idan ba a dawo da malaman aikin ba tare da biyan haƙƙoƙinsu.

Lauyoyin nasu suka ce ba a taɓa biyan su albashi ba tun bayan ɗaukarsu aiki a 2019 tare da rarraba musu wuraren aiki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito lauyoyin na cewa: an sanar da korar tasu ne ta kafar yaɗa labarai kawai wadda kuma ta saɓawa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

Daga Amir sufi

Leave a Reply

Your email address will not be published.