Shin Idan Saurayina Yace Ya Fasa Aurena Zan Iya Kaishi Kotu A Dokar Najeriya?

ME AKE NUFI DA BREACH OF PROMISE TO MARRY ?


“Breach of Promise to Marry” shine kayi ko kiyi alkawarin aure da abokin soyayyar ka/ki daga baya kuma dayan Ku ya saba wannan alkawarin. Duba Shari’ar Ezennah vs Atta (2004) 2 S.C.(Pt II) pg 75.

IDAN YAKI AURE NA ZAN IYA KAISHI KOTU A DOKAR NAJERIYA?

Ba wai kashe shi ko illata shi zakiyi ba dan haka ka iya jawo miki dauri, duba Shari’ar Victoria Alonge Vs. Roland Nna.

Idan daya yace ya fasa yin auren bayan kuma da yayi alkawarin auren to wanda aka sabama alkawarin zai iya zuwa kotu domin Neman hakkinsa, karkashin Matrimonial Causes Act, 1990, ko Islamic Law ko kuma Customary Law.

Duba Shari’ar Mabamije vs Otto (2016) LPELR 26058(SC) inda ta nemi ya biya ta diyyar Naira Miliyan Biyu, da kuma Shari’ar Uso Vs. Iketubosin [1975] WRNLR 187, da Shari’ar MARTINS Vs ADENUGBA (1946) 18 N.L.R 63.

Amma fa soyayya kawai ba tare da yin wannan alkawarin ba koda kun Shekara 10 a tare ba zai sa a kirashi Breach of Promise to Marry ba, duba Sharia’ar EZEANAH Vs. ATTA (2004) 7 NWLR (PT. 873) 468.

TO YAYA ALKAWARIN AUREN YAKE?

Alkawarin auren zai iya kasantuwa ta hanyoyi da dama, daga cikin su sun hada da:
1• Bata Zobe.
2• Tura Magabatan ka.
3• Kai Kudin Aure.
4• Kai kayan Lefe.
5• Yi a Rubuce.
6• Ka fada mata da Baki.
7• Da dai duk wani Abu wanda al’adar Ku ko addinin Ku ya dauke shi a matsayin ka tabbatar mata cewa auren ta zakayi.

Idan a cikin wadannan abubuwan Dana ambata a sama ba’a samu ko daya ba to alkali zai iya amfani da shaidar mutanen gari wurin yarda da cewa kayi mata alkawarin aure ko bakayi ba, ba dole sai ya fada mata da Baki ko kuma sunyi a rubuce ba. Duba Shari’ar Aiyede vs Norman –William (1960) LLR 253.

Wadannan kadan kenan daga cikin abubuwan da suke tabbatar da cewa kayi mata alkawarin zaka aure ta.

TO IDAN NA KAISHI KOTU TILASTA SHI ZA’AYI YA AURE NI?

A’a, idan kika kaishi kotu alkali ba zai tilasta masa ya aure ki ba, bayan kuma ya daina son ki, abinda alkali zaiyi shine; Na farko ya tabbatar da shin dagaske ma akwai soyayya a tsakaninku, idan ya tabbata daganan Kuma sai ya binciki gaskiyar abinda kika fada cewa ya yimiki alkawarin aure yanzu Kuma ya fasa, idan ya tabbatar da hakan to zai sa ya biyaki tara ne (Damage). Kuma alkali yakan kalli abubuwa Kamar haka wajen biyan ki tarar ko Damage:
1• Kudaden duk da kika kashe sakamkon fasa auren ki da yayi. Misali: Kudin da kika kashe wajen yin dilka, Wedding Gown, lalle, kitso, Invitation Card, Anko, Sarka, dan kunne, gyaran gashi, Kwalliyar da kikayi, da sauran su.
2• Ta bangaren lafiyar ki:
Zai biyaki kudaden da kika kashe sakamakon ciwon da kikayi, sannan zai biyaki kudin ciwon da shine sanadiyar samuwar shi a gunki, zai biyaki kudin damuwar da ya saka ki, zai biyaki kudin kunyata ki da yayi, sai kudin bakin cikin da ya saka ki a ciki da sauran su.
3• Zai biyaki kudin bata miki Lokaci da yayi, damarmakin ki da yasa kika rasa, da sauran su.
Dan haka duk wacce ta samu irin wannan matsalar kai tsaye ta tuntubi babban lauya masanin Shari’ah wato
Barr Na’Allah.

Shehu Rahinat Na’Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *