Ilimi

Tasiri Da Amfanin Karatun School Of Nursing Gare Mu a Yanzu (003)

Spread the love


Da yawan mutane basu fahimtar cewar, ɓangaren Nursing wani muhimmin ɓangare ne, da ba’a Najeriya kaɗai ba, har a duniya ma baki ɗaya, kowacce ƙasa an keɓance ɓangaren karatun Nursing a matakai daban-daban, bugu da ƙari kuma, ya kasu zuwa ɓangarori daban-daban, gwargwadon ɓangaren da ɗalibai suka samu ƙwarewa, ba kuma anan ya tsaya ba, cibiyoyin lafiya na ƙasa masu zaman kansu, da cibiyoyin lafiya na duniya, suna martaba ɓangaren karatun Nursing a School Of Nursing, da Jami’o’i, inda kuma ɗalibai a ko yaushe su ke samun damarmakin ƙaro karatu, ko sabon course a ɓangaren Nursing, yanzu a Najeriya, Schools Of Nursing suna cikin jerin makarantun gaba da Sakandire masu muhimmanci, da ake kulawa da su, kuma wani ɓangare ne da idan ɗalibai su ka yi, ba sa rasa aiki, a wani lokacin ma sai sun zaɓa.

Wasu Daga Cikin Nau’ikan Ma’aikatan Jinya a Najeriya (Nurses) :

1.Certified Nursing Assistant (CNA).

  1. 2.Licensed Practical Nursing (LPN).

3.Licensed Vocational Nursing (LVN).

  1. 4.Registered Nurse (RN).
  2. 5.Public Health Nurse.
  3. 6.Nurse Educators.
  4. 7.Maternal And Child Care Nurse.

•√Certified Nursing Assistant; (CNA) : Yawanci su na aiki a ƙarƙashin kulawar kai tsaye, na ma’aikatan jinya, kuma su na bayar da kulawar farko kai tsaye ga marasa lafiya, kafin Nurse ko Likita.

Ana ƙiran su kuma da; ”Nurse’s aid” wato masu taimaka wa Nurses, wajen gudanar da ayyukan su, da kuma kulawa da marasa lafiya, kuma ana ɗaukar su ne, a matsayin kashin ƙananan ma’aikatan jinya, wanda suke kan samun horo, ko kuma wanda suka samu horo na ɗan lokaci.

•√Licensed Practical Nurse; (LPN): Wannan rukunin na ma’aikatan jinya, kan gudanar da wasu ƙananan gwaje-gwaje ga marasa lafiya, kamar; gwajin hawan jini, yanayin zafin jiki da bugun zuciya, har ila yau sukan kasancewa daga cikin masu lura da marasa lafiya, har da yanayin karɓar magani da sha, da kuma cin abincin su, LPN suna aiki ƙarƙashin manyan likitoci, ko manyan ma’aikatan jinya, da ke tare da su.

•√Registered Nurse; (RN) : Ma’aikatan jinya ne, da su ka samu tabbacin ƙwarewa ta musamman, akan kula da marasa lafiya, tare da basu dukkanin taimako na lura da rashin lafiyar, da kuma inganta hanyoyin samar da lafiya, RN Nurses, sun kammala karatun Associate Degree in Nursing (ADN), wato General Nursing (GN), a School of Nursing, kuma a ƙarshe, su ka samu lasisin zama Nurse, daga hukumar ”Nursing And Midwifery Council of Nigeria (NMCN)”, bayan haye jarrabawowi da aka shirya, idan dai ɗalibai ba School of Nursing za suka yi ba, to hanyar zama Registered Nurse ita ce: Dole ɗalibi ya yi karatun Nursing a Degree.

RN Nurses, su na ba da haɗin kai, da kula da marasa lafiya, ilmantar da marasa lafiya, da jama’a, game da yanayin kiwon lafiya daban-daban, su na kuma taimakawa wajen, samar da kyakkyawan yanayi, da goyon baya ga marasa lafiya, da iyalansu.

RN Nurses, su na taka muhimmiyar rawa, a fannin kiwon lafiya, su ne kan gaba, a cikin ma’aikatan kiwon lafiya, ana ganin su a matsayin masu kulawa na farko, kuma suna da dangantaka da marasa lafiya sosai, domin kula da lafiya.

•√Public Health Nurse; Ma’aikatan jinya, na kula da lafiyar jama’a, sun ƙunshi mafi girman ɓangaren ma’aikatan sashen kiwon lafiya, kamar yadda Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ke yawan ambatawa, Ma’aikatan jinya na jama’a, su na shiga sahun gaba a ɓangaren rigakafi, ilimantarwa da bayar da shawarwari, kan batutuwan kiwon lafiya daban-daban, na iyali da ɗai-ɗaikun mutane.

Kuma, su na aiki tare da manyan cibiyoyi, ko hukumomi, domin shirin daƙile wasu cututtuka, ko rigafi, ayyukan su yawanci ya shafi inganta lafiyar al’umma, da aminci, da haɓɓaka damar samun lafiya, ga iyalai, hakanan ma’aikatan jinya, na lafiyar jama’a, su na bincika abubuwan da ke cikin muhalli, waɗanda za su iya shafar lafiyar al’umma, domin wanzar da gyara ta fuskar sha’anin lafiya, magance ƙalubalen lafiyar zamantakewa, gina daidaiton lafiya, da yiwa al’umma hidima, yawancin lokutan aiki, ana iya tsinkayar su suna ba da gudunmawa mai ƙarfi, a rayuwa, ta fuskar gangar jiki, da kuma gina bunkasar hankali ”intellectual development”, musamman ga yara ma su tasowa.

•√Nurse Educators; Malaman ma’aikatan jinya, ma’aikatan jinya ne masu rijista, tare da ilimi mai zurfi, waɗanda kuma malamai ne, ko masu bincike a ɓangaren lafiya, suna aiki a matsayin malamai, a makarantun aikin jinya, da asibitocin koyarwa, su na kuma taimakawa wajen tsarawa, da jagorantar ma’aikatan jinya (na ɗalibai), ta hanyar samar da bayanai masu amfani, da bincike, da su ka shafi ilimin aikin jinya, tare da batutuwan da suka fito daga manhajar koyarwa, da fasaha a fannin aikin jinya, ƙwararru ne, kuma masu horas wa, akan Aikin Jinya, su na kuma lura, da sababbin tsare-tsaren da hukumar kula da makarantun Nursing ta ke fitarwa, a ko yaushe, Nurse Educators; kan zamowa fitila ko madubi, ga sauran Nurses, wajen basu horon ƙwarewa da kula da marasa lafiya, da kuma Aikin bayar da taimako na musamman, ga marasa lafiya.

å Maternal Child Care Nurse; Wannan rukunin galibin su mata ne.

Ma’aikatan jinya ne, masu kula da batun ɗaukar ciki, da wanzuwa cikin kulawa da lafiyar uwar, da kuma abin da ke cikin ta, tare da dangantakar rayuwar jarirai, da iyayensu mata, ta ɓangaren lafiyar su duka, an fi sanin su da ”Unguwarzoma”, ƙwararru ne a kiwon lafiya, wanda aka horar da su, don ba da kulawa mai mahimmanci da tallafi, ga mata, a lokacin ɗaukar ciki, naƙuda, da karɓar haihuwa, suna taimaka wa mata, wajen kasancewa cikin ƙoshin lafiya, a lokacin da su ke da juna biyu, ta hanyar kiyayewa da lura da tsarin jikin su, rubuta tsare-tsaren kulawa da gudanar da kula da haihuwa a asibitoci, kuma su na kula da mata da yara, bayan haihuwa su na taimaka wa mata masu shayarwa, da kuma koya wa mata (musamman iyaye), na farko; yadda za su riƙe, da kuma kula da jariran da su ka haifa.

Waɗannan sune kaɗan daga cikin nau’ikan ma’aikatan jinya iri-iri, da ake samu a Najeriya, akwai wasu da yawa waɗanda za mu faɗe su, a wani shirin.

Ɗaliban da su ke sha’awar zama ma’aikatan jinya, dole ne su mallaki abubuwan da ake buƙata, ko da ya ke abubuwan na canjawa, daga makarantun, amma babban abinda ake buƙata shi ne; mallakar kyakykyawan sakamako na matakin Sikandire (O’ Level), tare da mafi ƙarancin Credits biyar, a Ingilishi, Lissafi, Biology, Chemistry da Physics.

♦Makarantun da su ke siyar da Form, a yanzu haka:

•Kebbi State School Of Nursing Science – Yanzu haka tana siyar da Form ɗin ta, ga ɗalibai masu buƙata.

•School Of Health Technology Minna – ita ma tana siyar da Form ɗinta.

Wannan shiri ne na musamman, da ƙungiyar Arewa Students Orientation Forum, ta ke gabatar mu ku, musamman ga ɗaliban Science, domin cin moriyar ɓangaren Nursing.

Kaitsaye, za ku iya tuntuɓar mu, ta wannan lambar 08086251045, a WhatsApp.

A kowanne shiri, za mu ke zuwar muku da muhimman bayanai, da za su taimakawa ɗalibai, a ɓangaren.

MASU ƊAUKAR NAUYI :

AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM DA TALLAFIN JARIDAR MIKIYA.

08086251045

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button