Ilimi

Tasiri Da Amfanin Karatun School Of Nursing Gare Mu, A Yanzu (004)

Spread the love

å Shin da gaske ne karatun Nursing yana da wahala ?.

Karatun Nursing ya kasu kashi-kashi, daga matakin karatun Nursing a School/College of Nursing, zuwa matakin karatun Nursing a Degree na ɗaya, da na biyu, har zuwa na uku, kuma kamar yadda a shirin mu na baya mu ka zayyano wasu rabe-raben Nursing (wato ɓangarorin sa) yana da yawa ƙwarai.

Babu wani karatu mai sauƙi, idan karatun za a yi, amma kam Nursing ba baya yake ba wajen buƙatar ƙoƙari, da ƙwazon ɗalibai, a yau za mu duba wani ɓangare na ”Tsarin Karatun School Of Nursing” wato ”Study Structure and courses”.

Da farko, batun shiga aji na ɗalibai : a mafi yawan Nursing Schools, ana shiga class ne daga ƙarfe 8:00 na safe, zuwa 4:00 na yamma, kuma tsawon shekaru Uku, kowacce shekara ana yin Courses kamar haka:

♦Karatun da ake yi, a shekarar farko, wanda ake ƙira da ”INTRODUCTORY/FIRST YEAR COURSES”, ko Nursing 100, sune kamar haka:

1.Anatomy and physiology one.

2.Foundation of Nursing.

3.Introduction to primary health care.

 1. Introduction to Reproductive Health.
 2. Pharmacology.
 3. Microbiology.
 4. Psychology.
 5. Sociology.
 6. Applied Physics.

10.Applied Chemistry.

 1. English (General).
 2. Nutrition.
 3. I.C.T + General.

Waɗannan sune, wasu daga Courses ɗin da ake yi a aji ɗaya (Nursing 100), sai dai ana iya samun banbanci kaɗan a wasu Nursing Schools ɗin.

♦SECOND YEAR COURSES ( Nursing 200) :

Wannan shekarar, kusan ta fi wahala a cikin shekaru ukun, domin karatu ya fara nisa, amma kuma tana zama mai sauƙi sosai ga wanda suka dage suka yi karatu a shekarar farko :

 1. Anatomy and physiology.
 2. Nursing practice.
 3. Pharmacology.
 4. Reproductive Health.
 5. Primary health care.
 6. Biostatistics.
 7. Research Methodology.

8.Emergency and Disaster Nursing.

 1. MENTAL HEALTH/ psychiatric.
 2. Community Nursing.
 3. Introduction to medical surgical Nursing one.
 4. Introduction to medical surgical Nursing two.
 5. Integumentary system.
 6. Musculoskeletal system.
 7. Cardio vascular system.
 8. Respiratory system.
 9. Endocrine system.
 10. Genitor Urinary system.
 11. Gastrointestinal system.
 12. Medical sociology.
 13. Dietetics.

Waɗannan su ne standard courses na Nursing 200, ko da yake ana samun banbanci kaɗan, tsakanin makaranta zuwa makaranta.

♦FINAL YEAR COURSES (Nursing 300) :

 1. Anatomy and physiology (3).
 2. Pharmacology.
 3. Nursing practice.
 4. Reproductive Health.
 5. Community Health Nursing.
 6. Research Methodology.
 7. Emergency and Disaster Nursing.
 8. Mental health.
 9. Central nervous system.
 10. Gastrointestinal system.
 11. Special senses/organ.
 12. Management.
 13. Health economic.
 14. Geriatric/ gerontology.
 15. Entrepreneurships (General).
 16. Waɗannan da mu ka zayyano, wasu daga ciki ne (basu kenan ba), kuma ana iya samun banbanci kaɗan, daga makaranta zuwa makaranta.

Ana yin sati 46 ne a shekara, wato Semester biyu kenan, amma yanzu a wasu makarantun an mayar da shi Sati 42 (42 weeks).

Kowacce Semester (21 weeks kenan) ga yadda tsarin yake kasancewa:

Lakca – Sati goma sha biyu (12weeks lectures).

6 weeks – clinical Posting.

1 week – Revisions.

1week – Exams.

1 Week – Vocation.

Wannan tsarin ma yana sauyawa daga makaranta zuwa makaranta, musamman in an samu banbancin jiha, wannan mun yi nazari ne akan wasu makarantun Nursing kaɗan.

Lokutan Admission: Wannan ma ya danganta ne da makarantar, amma mafi yawan Nursing Schools a Kano, ana yin admissions ne a October (na basic students nurses), sai kuma April (Midwives), ko da yake, ana samun sauyi gwargwadon yadda shekarar tazo, amma dai duk wata Nursing School da ta fara sayar da Form ɗinta na shiga, za mu dinga sanar da ku.

Admission requirements, da ake buƙata domin shiga School Of Nursing:

 1. Birth certificate (saboda ba a son mutum ya yi ƙasa da shekaru 16).
 2. Primary certificate.
 3. Secondry testimonial.

4.State Indigent Certificate, sometimes suna cewa a kawo na Local Government, saboda wasu ana biyan allowance duk wata.

 1. S.S.C.E Result – Wanda ya haɗa
  English, Maths, Biology, Chemistry da physics.

Wannan shiri ne na musamman, da ƙungiyar Arewa Students’ Orientation Forum ta ƙirƙiro, akan makarantun mu na Nursing, saboda taimakawa ɗalibai a ɓangaren, wajen samun admission, da dukkan sauran bayanai.

Muna yin wannan rubutun ne, da taimakon ɗalibin School Of Nursing Madobi, RN. MUKHTAR NAZIRU HAMZA, wanda shi ne ya samar mana da mafi yawan bayanan.

MASU ƊAUKAR NAUYI :

AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM DA TALLAFIN JARIDAR MIKIYA

08086251045

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button