Ilimi

Tasiri Da Amfanin School Of Nursing Gare Mu A Yanzu (005)

Spread the love

Babu shakka cewar, ɓangaren Nursing yana da abubuwa da yawa daya ƙunsa, kuma bugu da ƙari, ɗalibai za su so sanin wasu ɓangarori daga Ciki; a wannan shirin mun jero wasu muhimman batutuwa guda goma sha ɗaya (11), na tsarin karatun Nursing.

Wasu daga cikin ɗumbin kwasa-kwasan bai ɗaya (general), waɗanda ɗaliban nursing za su ci karo da su da zarar sun fara karatun Nursing:

  1. Nursing Foundamentals; Wannan galibi yana zuwa ne a First Semester (ta farkon shekara), inda za a yi bayanin abunda ake nufi da zama ɗaliban sanin makamar aikin jinya, yadda aikin kiwon lafiya yake, da matsayin ma’aikatan jinya a matakin ƙasa. Ana mayar da hankali kan koya wa ɗaliban muhimman abubuwan kulawa da haƙuri, baya ga ƙwarewar aikin jinya, har ila yau da yadda ya kamata ɗaliban su kasance. Wannan kwas ɗin na iya samun sunaye daban-daban a makarantu mabanbanta, kamar “Nursing 101” ko “Introduction to Nursing”, amma duk ka abu ɗaya ya ke koyarwa.

Wannan muhimmin batu ne a karatun Nursing, saboda shi ne ke kafa harsashin duk sauran ɓangarorin karatun na Nursing, hakanan ya na bawa ɗalibai ƙarin fahimtar ayyukan jinya daban-daban, wanda ke taimaka mu su wajen tabbatar da ko aikin jinya shi ne aikin da ya dace a gare su, ko a’a, inda kuma za a ƙarfafa gwiwar ɗaliban domin yin aiki tsakani da Allah.

2.Physiology; Physiology shi ne nazarin jikin mutum, da yadda ya ke aiki, ɗaliban Nursing za su koyi sanin sunaye da ayyuka na sassa daban-daban na jiki, da gaɓoɓi, da yadda duk su ke aiki a jikin ɗan Adam, da kuma nau’o’in cututtuka da raunuka daban-daban. Wannan yawanci ɗaya ne daga cikin batutuwa da ake koya wa ɗaliban nursing, kuma ya haɗar da batutuwa masu mahimmanci don kare lafiyar ma’aikatan jinya da amincin su, kamar yadda ake ɗagawa da motsa marasa lafiya cikin aminci, Physiology kuma yana tabbatar da cewa ma’aikatan jinya da sauran ƙwararrun masana kiwon lafiya, su na amfani da kalmomi iri ɗaya don bayyana yadda batutuwa suke, don haka ƙwarewar wannan yana taimakawa wajen tabbatar da ingantacciyar sadarwa, da bayanin kula na manyan likitoci, wannan ya sa ya zama muhimmin ɓangare na koyarwar ɗaliban nursing.

3.Introduction to Psychology and Mental Health;

Ilimin halayyar ɗan Adam,
ya ƙunshi ƙa’idoji da ayyuka na ilimin halin mutum, kuma yana taimaka wa ma’aikatan jinya su fahimci ilimin halin ɗan adam da yadda ake amfani da ilimin a matsayin ma’aikatan jinya, da mai lura da marasa lafiya ta fuskar ɗabi’a. Batutuwan sun haɗar da fahimtar yadda mutane su ke tunani, da yanke shawara, da kuma aiwatarwa. Ilimin halayyar majinyaci, da kuma yadda yake mu’amala, don sanin yadda za a iya shawo kan matsalar lafiyar sa, wannan kuwa ya haɗa da halayyar majinyata yara, da manya ko tsofaffi, da kuma irin nau’in jinyar
da ta shafi lafiyar ƙwaƙwalwa.

Wannan kwas ya shafi yanayin lafiyar hankali, da jiyyarsu, da kuma la’akari na musamman game da ɗabi’un da ke da alaƙa da kula da marasa lafiya, masu yanayin taɓin hankali.

Lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa, su na da alaƙa da juna, don haka wannan kwas yana da muhimmanci sosai, saboda yana bawa ma’aikatan jinya damar ba da kulawa sosai, ga marasa lafiya.

Nazarin ilimin halin ɗan Adam, zai iya taimaka wa ɗalibai wajen fahimtar halayyar marasa lafiya, da kuma su a karan kan su.

4.Microbiology;
Microbiology shi ne nazarin ƙananan ƙwayoyin cuta, duk wata halitta da ta yi ƙanƙantar gani da ba za a iya ganinta ba tare da na’urar microscope ba, ciki kuwa har da kwayoyin cuta, da wasu nau’in fungi. Wannan ma wani kwas ne da ake buƙata a makarantar koyon aikin jinya, ko kafin shiga, domin fahimtar irin rawar da ƙananan ƙwayoyin cuta ke takawa a lafiyar ɗan adam, kuma ya zama dole a fahimci sauran fannonin kiwon lafiya da dama, batutuwan da su ka haɗar da; ƙananan ƙwayoyin cuta waɗanda ke haifar/taimakawa wajen hana cututtuka yaɗuwa, da ƙananan ƙwayoyin cuta waɗanda ke haifar wa ɗan adam wasu cututtukan. Wannan kwas baki ɗaya ya shafi aikin lab ne da aikin aji, kuma domin samun cikakken horo, shi ma yana cikin muhimman kwasa-kwasai da ake yi a karatun nursing, saboda yadda ƙwayoyin cuta su ke taka muhimmiyar rawa ga lafiyar ɗan adam.

  1. Gerontology; Gerontology shi ne nazarin tsufa; Tsufa wani tsari ne da ya ke zuwa a hankali, ci gaba da canjin yanayi wanda ke farawa tun farkon shekaru, da shekarun tsakiya, yawanci ƙarfin jiki yana fara raguwa ne a hankali, Gerontology shi ne nazarin tsarin tsufa, gami da canje-canjen jiki da tunani, da zamantakewa. Ana amfani da bayanin don haɓɓaka dabaru da shirye-shiryen inganta rayuwar tsofaffi da lafiyar su. Ilimin gerontology ga ɗaliban Nursing a Nursing Schools, ya haɗar da batutuwan yanayin da ke da alaƙa da tsufa, ilimin halin ɗan adam a ya yin tsufa, yadda ake mu’amala da tsofaffi majinyata, Gerontology yana cikin manyan kwasa-kwasan Nursing, saboda muhimmiyar rawar da ma’aikatan jinya ke takawa, wajen ba da kulawa ga tsofaffi.

Wannan babban darasi ne ga ma’aikatan jinya, waɗanda ke shirin ƙwarewa a fannin ilimin gerontology, baya ga likitocin yara da masu haihuwa, tsofaffi su na da yawan majinyata, don haka ikon fahimtar buƙatun su da samar da ingantaccen kulawar jinya, yana da mahimmanci, kuma aikin lada ne sosai, baya ga samun nasarar ɗalibai na zama Nurses.

  1. Pharmacology; Pharmacology shi ne nazarin magunguna, darussan aikin jinya a cikin ilimin harhaɗa magunguna su na mai da hankali ne kan sarrafa magunguna, gami da yanayin tasirin su ga majinyata, da kuma yadda za a tsara shan magungunan, baya ga koyo kan magunguna da yadda su ke aiki, ɗalibai za su san muhimman bayanan magunguna, ko da kuma ba za su rubuta magunguna ba, dole ne su fahimci tushen ilimin harhaɗa magungunan, don tabbatar da amincin marasa lafiya, da amsa tambayoyin su akan maganin.

7.Women and infant Health; Lafiyar mata da jarirai, ta shafi lafiyar mata, lafiyar ciki da haihuwa, da inganta lafiyar jarirai, wannan ya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da kulawar jinya kaitsaye, ga mata masu juna biyu, da kuma bayan haihuwa, dan samar da rigafin inganta lafiyar jarirai. Wannan darasi ne na musamman, wanda ɗalibai ke samun horo a cikin tsarin karatun su na makarantar Midwifery.

  1. Community and Environmental Health;

Kula da muhalli, reshe ne na lafiyar jama’a kai tsaye, da ake koya wa ɗalibai a nursing, kuma ya shafi lura da yadda al’umma da muhalli ke shafar lafiya, da yadda ake haɓɓaka lafiya a cikin al’ummomi da muhallai daban-daban, ɗalibai za su yi nazarin abubuwan da su ka haɗar da amincin al’umma, gurɓataccen yanayi da tasirinsa ga lafiya, da wayar da kan al’umma kan lafiya, a cikin birane da karkara, a matsayin, wani ɓangare na wannan kwas, ɗalibai za su yi nazarin al’ummar su, da abubuwan da ke tasiri ga lafiyarta.

A matsayin ma’aikatan lafiya ma’aikatan jinya, su na daga cikin mutane na farko da su ke hulɗa da mutane masu buƙatar bayanai, kan illolin muhalli ko cututtuka masu yaɗuwa, fahimtar tasirin al’amuran al’umma da muhalli akan kiwon lafiya, babban jigo ne ga ɗaliban Nursing.

  1. Care Transition;

Wannan kuma ana koyawa ɗalibai tsarin canja wurin marasa lafiya ne, daga wani yanayin kiwon lafiya zuwa wani, ko fitar da marasa lafiya domin tsaftace wurare, kuma
ya ƙunshi wasu batutuwa da su ka haɗar da haɓɓaka kiwon lafiya, rage haɗari, da ayyukan kula da lafiya.
Dole ne ɗaliban ma’aikatan jinya su fahimci yadda ake canja wurin mahimman bayanan marasa lafiya, ciki kuwa har da bayanan magani, da sauransu.

10.Population Health;
Wannan kwas ɗin yana bincika bayanai da matakai a tsarin kiwon lafiya, da ƙa’idojin zamantakewar muhalli, a tsarin lafiyar al’umma, kuma ya ƙunshi batutuwa kamar su epidemiology, haɓɓaka kiwon lafiya, da kuma ƙara samun damar kula da lafiya a cikin al’umma, a wannan kwas, ɗalibai za su koyi abubuwan zamantakewa da ke shafar kiwon lafiya da tsarin sa,
baya ga tsare-tsaren lafiyar jama’a, kamar allurar rigakafi.

Fahimtar waɗannan abubuwan da yadda su ke aiki, yana taimakawa ɗalibai fagen haɓɓaka lafiya a matakai daban-daban, wanda kuma abu ne mai mahimmanci matuƙa ga ɗalibai a aikin kulawa, ko dabarun kiwon lafiya.

11.Clinical Theory;

Yana koya wa ɗalibai ƙa’idojin ilimin likitanci da jiyya, da kuma yadda ake tsara ayyukan likitanci da na jinya ɗin, kamar gwadawa, tare da amfani da su. A cikin waɗannan darussan, ɗalibai za su koyi yadda nau’ikan magunguna daban-daban su ke, da yadda za su kula da fannonin kiwon lafiyar da su ka shafi aikin jinya, baya ga yadda ake lura da ƙa’idojin zuwa aikin na yau da kullum. Kwas ɗin yana taimakawa ɗalibai wajen yin tunani tare da da basu dabaru game da lafiya da kiwon lafiya, kuma yana da mahimmanci musamman ga ɗaliban.

MASU ƊAUKAR NAUYI : AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM, DA TALLAFIN JARIDAR MIKIYA.

08086251045.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button