Ilimi

Tasiri Da Amfanin School Of Nursing Gare Mu A Yanzu (006)

Spread the love

Akwai banbanci sosai, ta fuskar makarantun da ke gudanar da karatun nursing, galibi makarantun da ake nursing su ne Schools Of Nursing, Colleges Of Nursing, sai Diploma, da kuma makarantun da su ke ƙarƙashin Asibitocin koyarwa (Teaching Hospitals). Galibi akwai muhimman abubuwan da ya kamata a fayyace wa ɗalibai, wanda hakan shi ne manufar wannan program ɗin.

A wannan program kashi na shida (6), za mu yi nazari ne akan banbancin da ke tsakanin Basic Nursing, da ND Nursing.

Babban banbanci tsakanin ND Nursing, da Basic Nursing shi ne cewar; waɗanda su ka kammala Basic Nursing za a basu Testimonial ne kaɗai, sai kuma Professional license da shima za a basu daga babbar hukumar da ke kula da makarantun, wato ‘Nursing And Midwifery Council Of Nigeria’.

Yayin da waɗanda su ka kammala ND Nursing, za su samu shaidar kammala Diploma ta ND a nursing, da kuma shaidar Nursing And Midwifery Council Of Nigeria.

ND Nursing program ne na shekaru huɗu (4), ba tare da katsewa ba, idan ɗalibai su ka fara da ND Nursing, za su cigaba da HND Nursing, yayin da Basic Nursing kuma, shekaru uku (3) ne.

ND da HND Nursing, su na zuwa internship na shekara ɗaya, domin samun horo na musamman.

Waɗanda su ka kammala ND Nursing, da HND Nursing, su na tafiya hidimar ƙasa ta NYSC na shekara 1, yayin da waɗanda su ka kammala Basic Nursing basa zuwa.

Waɗanda su ka kammala karatun Nursing na ND da HND, za a ba su lasisin ƙwararru guda biyu, wato Registered Nurse (RN), da Registered Midwife (RM), ko Registered Public Health Nurse (RPHN).

Yayin da waɗanda su ka kammala karatun Nursing, na Basic Nursing, Registered Nurse (RN) ne kaɗai za a basu.

Bayan kammala ND da HND Nursing, ɗalibai za su iya yin Postgraduate Diploma in Nursing (PGD in Nursing).

Amma waɗanda su ka kammala karatun Basic Nursing, dole ne su fara yin Digiri na farko a Nursing (BNSc), kafin su iya cigaba zuwa Postgraduate Diploma in Nursing (PGD).

Sai dai, a yanzu ana yunƙurin mayar da Basic Nursing baki ɗaya ya koma ND Nursing.

Ta fuskar ƙwarewa kuwa, kowanne ɓangare su na samun ƙwarewa sosai a gudanar da ayyukan su, sai dai kawai waɗanda su ka yi ND da HND Nursing dole ne sufi samun horo, saboda banbancin yawan shekarun da aka ɗauka ana yin karatun.

MASU ƊAUKAR NAUYI

ƘUNGIYAR AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM Da TALLAFIN JARIDAR MIKIYA.

08086251045

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button