Ilimi

Tasiri Da Amfanin School Of Nursing Gare Mu, A Yanzu, Kashi Na Goma (010)

Spread the love

A Amurka, da wasu ƙasashen Turai, masu digiri na ɗaya, da na biyu, na komawa kwalejojin nursing, domin samun horo, a matsayin RN.

A wannan shirin, za mu bibiyi tasirin karatun jinya a duniya, tare da wasu ɓangarorin sa, gami da wasu daga cikin rabe-raben sa, da kuma batu akan ko Nurse zai iya zama Likita ?.

Kowanne Likita, yana buƙatar nurse, domin ƙarfafa Aikin sa, tare da samun taimako, ko da ya ke kowanne Likita Nurse ne, Amma ba kowanne Nurse bane Likita. Abin da kawai mu ke son mu sani shi ne; matakin zurfin ilimin da Nurses su ke da shi, ba kowanne Nurse bane a matsayin kowanne, kuma akwai rabe-raben ƙwarewa, da inda kowanne yafi ƙwarewa. Amma dai, an yi ittifaƙin cewar, Nurses da yawa daga baya, su na rikiɗewa su zama manyan Likitoci, ta hanyar zuwa ƙaro karatu, a fannin likitan cin, kai tsaye!.

Ku tabbata cewa, damar yin aiki a gare ku za su yawaita, a cikin shekaru masu zuwa, muddin kun ɗauki matakan da su ka dace, da ilimin ku na Nursing daga makarantar jiyya, da aka amince da ita, hakan zai ba ku damar samun ɗumbin ayyukan yi, a wannan fanni mai girma.

Aikin jinya, wani fanni ne mai matuƙar mahimmanci, kuma wanda ke cike da damarmaki, a cewar Ofishin ƙididdigar Ma’aikata na Amurka, ”babu wani rukuni, na Aikin lafiya a duniya, da Nurses basa taka rawar gani, tare da taimakawa”, kamar yadda American Association of Colleges Of Nursing(AACN) ta sha nanatawa, inda ta ke shawartar jama’ar duniya baki ɗaya, da su dage wajen neman Ilimi a school of Nursing. Har ila yau, AACN ta hakaito labaran da ke nuni da cewa, a yanzu Amurkawa da yawa, kan mayar da hankali ne a ɓangaren, ba tare da lura, ko la’akari da matakin karatun su na Degree, Masters, ko PhD ba, inda da yawan su kuma ke iƙirarin cewa, ya kamata su samu ilimi a ɓangaren kula da lafiya a matakin farko, a ƙalla su samu horo a school of Nursing, domin kula da iyalan su.

Batun kiwon lafiya, shi ne abu mafi girma, cikin sauri a duniyar yau, tare da ƙarin damarmakin ayyuka, fiye da kowane fanni.

Ma’aikatan jinya (Nurses) kuma, su ne mafi yawan kaso na ma’aikatan kiwon lafiya, a duniya baki ɗaya.

Buƙatar ma’aikatan jinya, tana daɗa yawa akai-akai, saboda yadda ake buƙatar su, a kusan dukkanin sassan ma’aikatun kiwon lafiya.

Nurses, ko ma’aikatan jinya : a ko yaushe mutane kan gaza rarrabewa, ko da ya ke a shirye-shiryen da suka gabata, mun hakaito wasu ɓangarorin specialization a Nursing, kamar irin su, Cardiology nursing, Geriatrics nursing, Holistic sciences, Oncology,
da sauran su.

A wannan jerin, za mu iya ganin wasu daga cikin rabe-raben ma’aikatan jinya, yanayin ƙwarewar su, da ma ayyukan su :

√• Advanced Practice Registered Nurse (APRN) : APRNs su na kula, da kuma tantance marasa lafiya, kuma su na iya rubuta magunguna. Akwai nau’ikan APRNs da yawa, kuma duk su na samun horon ci-gaban aikin Nursing, tare kuma da faɗaɗa matsayi, fiye da registered Nurse. Ɗalibai su na buƙatar ƙwarewa, da yin kwasa-kwasai na musamman, domin zamowa APRNs.

å Critical Care Nurse(CCN) :
Su ma ma’aikatan jinya ne masu rijista, waɗanda ke aiki a rukunin kulawa ta musamman mai zurfi, su na ba da kulawa mai mahimmanci ga waɗanda ke da cututtuka masu buƙatar kulawa ta musamman, ko raunuka masu tsanani, waɗanda ke buƙatar kulawa. Tare da wannan, yawancin ma’aikatan jinya, a wannan ɓangaren ana buƙatar su samu Bachelor’s in Nursing (BSN), bayan school of Nursing.

√• Family Nurse Practitioner (FNP) : Ma’aikatan jinya na Iyalai, waɗanda aka fi sani da FNPs, su na aiki a matsayin masu ba da kulawa na farko, ga marasa lafiya, su na kuma tantance marasa lafiya, dai-daita tsare-tsaren jiyya, rubuta magunguna, da kuma kasancewa ƙwararru wajen bayar da shawarar tsara iyali, ta fuskar lafiya.

å Geriatrics Nursing (GN) :

Ma’aikatan jinya na Geriatric RNs ne, waɗanda ke kula da tsofaffi marasa lafiya yawanci, waɗannan marasa lafiya su na da rashin lafiya sosai, ko saboda shekarun su. Ma’aikatan jinya na Geriatric, na iya aiki a gidajen marasa lafiya, gidajen jiyya, da Asibitoci, domin bayar da kulawa ta musamman, ga tsofaffi masu yawan shekaru.

√•Home Health Nurse(HHN) : Yawanci ma’aikatan jinya ne masu rijista, waɗanda ke aiki kai tsaye a gidajen marasa lafiya, kuma marasa lafiyar na iya zama tsofaffi, naƙasassu, ko jinya ta yau da kullum, ko kuma masu naƙudar gaggawa, da ta kama su a gida, ko dai marasa lafiyar da a kowane hali, ba za su iya rayuwa, ba tare da kulawar ma’aikaciyar jiyya ba.

√• Labour and Delivery Nurses (LDN) : Wannan nau’in ma’aikatan jinya, su na aiki a Asibitoci, a sashen OB/GYN, kuma su na iya aiki a cikin sirri (OB/GYN), haka zalika, su na taimaka wa Iyaye mata, wajen haihuwa, kuma su na ba da tallafi ga jariran da aka haifa, da kuma taimakawa, wajen kula da uwa da jariri, bayan haihuwa.

√• Pediatric Nurse(PN) : Wannan nau’in ma’aikatan jinya, su na aiki ne a ɓangaren jarirai, yara, da matasa (tsakanin shekarun 0 zuwa 19), akan kulawa na farko, da na rigakafi. Ma’aikatan jinya na wannan ɓangaren, sukan yi aiki a asibitoci, cibiyoyin kula da marasa lafiya, makarantu, da ma ayyuka masu zaman kansu, tare da likitan yara.

√• Managed Care Nurse (MCN) : su ne RNs ɗin da ke aiki, a sashen marasa lafiya, waɗanda ke buƙatar kulawa ta dogon lokaci, waɗannan marasa lafiya su na da yanayi na buƙatuwar tallafawa lafiyarsu, yau da kullum, kuma su na buƙatar kulawa ta musamman, ga sauran rayuwar su.

√• Military Nurses(MN) : Ana buƙatar ma’aikatan jinya ko yaushe a cikin sojoji, don kula da sojoji marasa lafiya, da sauran ma’aikatam da ke Aiki, tare da sojojin.

√• Neonatal Nurse(NN) : ma’aikatan jinya ne na jarirai, kuma su na aiki a sashen kulawa na Neonatal, ya yin da su ke kula da marasa lafiya, da jariran da ba su kai lokacin haihuwa ba, waɗanda ke buƙatar ci gaba da samun tallafin gudanar da rayuwar su, tare da kulawa.

√• Oncology Nurse (ON) : Ma’aikatan jinya na Oncology, su na aiki ne kai tsaye tare da ma su cutar daji, kuma su na aiki da ƙungiyar likitoci, don kula da marasa lafiyar da ke fama da cutar daji, ko kuma waɗanda ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.

√Physician’s Office Nurse : Wannan nau’in ma’aikatan jiyya, su na aiki a tare da likitan sirri ne. Sau da yawa su na aiki tare da ƙungiyar ma’aikatan jinya, mataimakan likita, da ma likitoci.

√• Psychiatric Mental Health Nurse Practitioner (PMHNP) : Waɗannan ƙwararrun ma’aikatan jinya nau’in APRN ne, waɗanda su ka ƙware a fannin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa. Don haka su na buƙatar ƙwarewa ta musamman, kuma ana iya samun PMHNP sau da yawa su na aiki a asibitoci, unguwanni, da gidajen gyaran hali.

√• Surgical RN (Nurses) : Babban aikin ma’aikatan jinya na wannan fanni shi ne; taimakawa likitocin fiɗa, a lokacin Aiki, ban da wannan kuma, ma’aikatan aikin jinyar na wannan ɓangare, su kan kula da marasa lafiya, kafin da kuma bayan tiyata.

√• Trauma Nurses (TN) : Ma’aikatan lafiyar mata, sun ƙware a fannoni kamar; OB/GYN, lafiyar haihuwa, rashin haihuwa, mammography, da ma lafiyar mata baki ɗaya. Kuma yawanci ana iya samun waɗannan ma’aikatan jinya a cikin ayyuka masu zaman kansu, na OB/GYN, da kuma sauran sassan ɓangaren.

Za mu dakata anan, mu haɗu a kashi na 11.

MASU ƊAUKAR NAUYI : ƘUNGIYAR AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM, DA TALLAFIN JARIDAR MIKIYA.

      08086251045

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button