Ilimi

Tasiri Da Amfanin School Of Nursing Garemu A Yanzu (001)

Spread the love

Wannan shirin kacokan, zai fi mayar da hankali ne ga ƴan’uwan mu ɗalibai mata, da kuma kaɗan daga cikin ɗalibai maza, domin fayyace batutuwa masu muhimmanci akan makarantun jinya da unguwarzoma (Nursing And Midwifery).

Karatun Nursing ko Midwifery, karatu ne da a ƙalla ake yinsa tsawon shekaru uku (masu albarka), domin kuwa akan samu waɗanda daga nan basu ƙara wani karatun ba ma, amma wannan ya riƙe rayuwar su a matsayin sana’a.

A wani bincike da cibiyar UNICEF ta gabatar a shekarar 2020, ta gano cewar har yanzu a Najeriya ana buƙatar ƙarin ma’aikatan jinya da unguwarzoma, domin taimaka wa manyan likitoci wajen kula da marasa lafiya!.

Karatun Nursing, saboda muhimmancinsa ne ya sanya aka ƙirƙiri School Of Nursing And Midwifery daban-daban a faɗin Najeriya, kuma a kowacce jiha.

Schools Of Nursing, makarantu ne keɓantattu da ɓangaren lafiya ya keɓe, inda aka ɗora wa hukumar “Nursing And Midwifery Council Of Nigeria” alhakin kula da makarantun na Nursing, babbar helikwatar hukumar tana Lagos, yayin da su ke da Ofishioshin shiyya-shiyya a wasu jihohin Arewa.

A wasu lokutan ɗalibai kan sha fama, kafin samun admission a waɗannan makarantu, amma manufar wannan shirin na ASOF shi ne taimaka wa ɗalibai domin samun Admission a makarantun Nursing, da kuma samar da ingantattun bayanai.

å Wasu daga cikin rabe-raben Schools Of Nursing:

SON; School Of Nursing (Basic).

SOMBP; Schools Of Midwifery Basic/Post Basic.

SOPN; Schools Of Post Basic Nursing Specialities.

DON; Depertment Of Nursing Science.

CMP: Community Midwifery Program.

CNP; Community Nursing Program.

Shekarun karatu : mafi yawan makarantun nursing ana yin karatun shekaru uku ne, kuma akan tura ɗalibai asibitoci domin neman ƙwarewa a fannonin da suka yi karatun, yayin da da zarar ɗaliban sun kammala, sukan samu ɓangaren dogaro da kansu ko su samu aiki a asibitocin gwamnati, ko masu zaman kansu, ko kuma a cibiyoyin sayar da magunguna (Patient Medicine Stores).

Ɗaliban da suka yi karatun nursing, kuma suka haye jarrabawar da ake shiryawa, suna zama RN (Registered Nurse), wato ma’aikacin jinya mai lasisi.

√• Wasu daga Cikin departments ɗin da ɗalibai ke samun damar yi a School Of Nursing :

Public Health Nursing.

Orthopaedic Nursing.

Paediatrics Nursing.

Anaesthetist Nursing.

Accident and Emergency Nursing.

Pre-operative Nursing.

Ear, Nose and Throat Nursing.

Burns and Plastic Nursing.

Cardiothoracic Nursing.

Occupational Health Nursing.

Intensive Care Nursing.

Nursing Administration.

General Nursing.

Kowanne ɓangare za mu dinga ɗaukar sa muna bayani, a cikin wannan shiri.

√• Yadda Ɗalibai za su shiga School Of Nursing har su zama RN:

• Siyan form na School of Nursing.

• Rubuta jarrabawar share fage (entrance examination).

• Halartar screening da interview exercise.

• Samun admission da rijistar fara karatu.

Samun sahalewar hukumar
Nursing and Midwifery Council of Nigeria, bayan yin jarrabawa, tare da samun makin da ake buƙata.

A cikin shirin, za mu ke lissafo Nursing Schools, tare da bayanin lokutan ɗaukar ɗalibai, da kuma hanyoyin da ake bi, domin samun admission.

Bugu da ƙari, za ku iya ajiye tambayoyin ku akan School Of Nursing, a Comments Box, ko kuma ku tuntuɓe mu ta WhatsApp : 08086251045.

A cikin bayanan kuma, za mu ke kawo ɓangaren da ɗalibai za su iya yi a HND, da kuma Jami’a, dukka dai a ɓangaren Nursing, da kuma irin damarmakin da ake samu sosai, dukka dai domin ƙarfafa gwuiwar ɗalibai su fahimci muhimmancin ɓangaren (musamman mata),
an samar da wannan Program ɗin ne dai, sabo da yawaitar Yajin Aikin ASUU, da yake shafar jami’o’i.

Masu Ɗaukar Nauyin Shirin

AREWA STUDENTS ORIENTATION FORUM DA HAƊIN GWIWAR JARIDAR MIKIYA

   08086251045

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button